Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Shugaba Yoweri Musevini Ya Zamo Shugaban Uganda Na 7 Yana Da Shekaru 81 Kuma Ya Shafe Shekaru 50 A Mulki
Published: January 19, 2026 at 9:17 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumomin Uganda sun maido da wasu layukan intanet na kasar cikin daren asabar a bayan da aka ayyana cewa shugaba Yoweri Museveni mai shekaru 81 da haihuwa ya lashe wa’adi na 7 a kan mulki, ma’ana zai shafe shekaru 50 da wani abu yana mulkin kasar.

‘Yan adawa dai sun yi watsi da sakamakon zaben da aka bayyana a zaman na bogi.

Da misalin karfe 11 na daren asabar mutanen kasar ta Uganda suka ce sun fara iya hawa kan intanet, inda wasu kamfanonin sadarwa na kasar suka aike da sako ga kwastomominsu cewa hukumomi sun ba su iznin maido da intanet, amma kuma su ci gaba da toshe hanyoyin hawa kan shafukan sada zumunci.

Hukumar sadarwa ta Uganda ta ce ta bada umurnin katse hanyoyin intanet ne domin dakile yada jita-jita da karairayi da yin magudin zabe. Amma ‘yan hamayya sun soki wannan, suna masu fadin cewa an yi hakan ne kawai domin garkame duk wani fanni na zaben domin tabbatar da cewa Museveni ne ya lashe shi.

A ranar asabar, hukumar zabe ta Uganda ta ce Museveni ya lashe zaben rana4 akhamis da kashi 71 cikin 100 yayin da babban abokin hamayyarsa Bobi Wine ya samu kashi 24 cikin 100.

Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya
Next Post: Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa

Karin Labarai Masu Alaka

Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa Afrika
PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa Afrika
Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
Farashin Mai Yayi Tashin Gwaron Zabi Afrika
Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika
  • Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya
  • Shugaban Amurka Zai Sake Aika Jirgin Yaki Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • An Kai Hari Kan Masu Hakar Ma’adanai A Kasar Mali Tsaro
  • Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
  • Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane Afrika
  • Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
  • Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.