Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya
Published: June 18, 2026 at 7:23 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sarkin Jaurowal dake Masarautar Pindiga, Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe, Comrade Ambassador Ibrahim Mu’azu Hassan, ya roƙi gwamnatoci a dukkan matakai su samar da muhimman kayan more rayuwa ga al’ummar da ke ƙarƙashinsa.

Yayin da yake Tattaunawa da Wakilin Amurka Ke Magana a jihar Gombe, sarkin ya roƙi shugabannin siyasa, masu hannu da shuni, da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu su tallafawa yankin ta hanyar sauƙaƙa samar da Hanyoyi, Cibiyoyin lafiya, da Makarantun ilimi.

Mu’azu Hassan ya bayyana damuwarsa kan halin da ababen more rayuwa ke ciki a yankin, musamman hanyoyi, wanda ya ce ya haddasa mutuwar akalla mata 5 da ba su samu damar samun magani a kan lokaci ba yayin da ake ɗaukarsu zuwa asibiti.

Ya yi kira ga gwamnatin Gwamna Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, Sanata Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, da Dr. Usman Bello Kumo ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Akko, Alhaji Abubakar Abdullahi Mai Wanka dan majalisa mai wakiltar Akko ta Yamma dasu shiga tsakani su magance matsalolin da al’ummar yankin ke fuskanta.

Sarkin ya kuma yi ƙorafi kan watsar da aikin gina Makarantar Junior Secondary School ta Jaurowal da aka shirya yinta kuma basuyi ba har yau, inda ya ce ginin ya tsaya shekaru 7 da suka wuce, ya kuma ƙara da cewa mazauna yankin suna fama da matsaloli wajen samun ingantaccen ilimi da lafiya.

Ya kara roƙon gwamnati ta ba yankin kulawa, ta kuma ƙirƙiri “Ward” saboda Jaurowal yana da kauyuka kusan 10, ciki har da Garin Jauro Jibir, Labarfito, Dongoru Karama, Felawa, Bakkiti, Pali, Lafiyawo, da Ardowu,Garin Yabano etc.

Duk da yawan jama’a da gudummawar da suke bayarwa ga karamar hukumar, ya ce al’ummar yankin ba su ci moriyar ayyukan ci gaba da ‘ya’yan dimokuraɗiyya ba har yanzu.

Mu’azu Hassan ya roƙi hukumomi masu dacewa su ba da fifiko ga bukatun yankin, su inganta rayuwar mazauna yankin ta hanyar samar da ababen more rayuwa da ayyukan cigaban al’umma.

A karshe yana addu’a ga kasar Pindiga Emirates da Garin Jaurowal jihar Gombe da Nigerian baki daya da Allah yabasu zaman lfy da cigaba mai dorewa.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa
Next Post: Makokin Ashura: An Gudanar Da Taron Tunawa Da Aliyul Asghar A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
Harkar Zirga Zirgar Jiragen Sama Ya Bunkasa A Kenya Afrika
Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna Labarai
Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka
  • Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
  • Kasar Spain Zata Bada Diyya Ga Iyalen Wadanda Da Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Kasa Labarai
  • Aikin Layin Dogon Kasar Uganda Zai Hade Kasar Da Tanzania Da Kwango Kimiya
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
  • Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.