Daga Mohamman Awwal Garba a Kamaru
Ƙungiyar ANNOUR ta tallafa wa yara kusan 500 daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi a birnin Douala na Kamaru, ta hanyar rabon kayan makaranta da kuɗinsu ya kai kimanin Francs CFA miliyan 5 da dubu 500.

An gudanar da shirin ne a filin waha na wasannin Olympics da ke Douala, domin taimaka wa iyalai wajen rage musu nauyin kuɗaɗen da ake kashewa wajen shirya yara zuwa sabon zangon karatu.
Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin El Hadj Aboubakar Bako Mandeng, Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiyar Musulmi ta yankunan Littoral da Kudu maso Yamma, tare da halartar wasu daga cikin sarakunan gargajiyar da ke cikin majalisar.
Ƙungiyar ANNOUR, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba El Hadj Zakari Yaou, ta shafe shekaru shida tana gudanar da shirye-shiryen tallafawa al’umma, musamman mutanen da ke cikin mawuyacin hali.
Shirin tallafawa yaran bai tsaya a Douala kaɗai ba. A makon da ya gabata, ƙungiyar ta kai irin wannan tallafi yankin Penja, yayin da take shirin faɗaɗa ayyukan zuwa Moutenguéné da Tiko.
Ana sa ran cewa jimillar yara kusan 1,000 a waɗannan yankuna za su amfana da shirin.
Ƙungiyar ta ce ta himmatu wajen ci gaba da shirye-shiryen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi, tare da ba da fifiko ga yara da iyalan da ke fuskantar matsalolin rayuwa.
Shirin ya samu yabo daga iyalan da suka amfana da tallafin, da kuma manyan baƙin da suka halarci taron a Douala, waɗanda suka bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na tallafa wa ilimi da jin daɗin al’umma.


