Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen
Published: July 4, 2026 at 4:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: July 4, 2026

An binne gawar tsohon shugaban Sashen Hausa na Gidan Rediyon Muryar Amurka (VOA), Leo Keyen, yayin da ‘yan’uwa, abokan aiki da abokan arziki suka yi masa bankwana tare da bayyana shi a matsayin ƙwararren ɗan jarida, shugaba nagari, kuma mai jajircewa wajen bunƙasa aikin jarida da raya matasa.

Marigayi Leo Keyen ya rasu ne a ranar 22 ga Yunin 2026, yana da shekaru 70 a duniya, bayan ya shafe kusan shekara goma sha ɗaya yana fama da cutar Parkinson’s Disease.

Da yake jawabi, ɗan’uwan marigayin, Injiniya Noel Keyen, ya ce rasuwar ta yi wa iyali da abokansa babban rashi, amma sun amince da hukuncin Allah.

Marigayi Leo Keyen ya yi aiki a cibiyoyin yaɗa labarai da dama, ciki har da NTA da JIB, sannan ya kasance Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP ta ƙasa a zamanin marigayi Solomon Lar. Haka kuma, ya taba zama Babban Daraktan Gidan Rediyo da Talabijin na Jihar Filato (PRTV) sau biyu.

Daga shekarar 2011 zuwa 2018, Leo Keyen ya jagoranci Sashen Hausa na VOA, inda ya faɗaɗa ayyukan rediyo, talabijin da kafafen yanar gizo, lamarin da ya ƙara yawan masu sauraro da masu kallo a Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi da sauran ƙasashe.

Wasu daga cikin shirye-shiryen da ya assasa sun haɗa da Dandalin VOA, Taskar VOA da kuma Tattaunawa, waɗanda suka mayar da hankali kan siyasa, shugabanci da harkokin tsaro.

Tsohon Shugaban Gidauniyar Horas da Ma’aikata ta ITF, Sir Joseph Ari, ya ce ƙwarewar Leo Keyen ta taimaka wajen samar da ingantattun labarai da shirye-shiryen da suka amfani al’umma.

Shi ma tsohon abokin aikinsa a VOA, Malam Sahabo Imam Aliyu, ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai adalci da nagarta, yayin da Hajiya Madina Dauda Nadabo ta ce Leo Keyen mutum ne da bai nuna bambanci tsakanin ma’aikatansa.

Baya ga aikin jarida, marigayin ya kasance mai ƙarfafa gwiwar matasa wajen shiga harkokin kasuwanci da dogaro da kai.

A nasa jawabin, Hon. Kefiano Kefas Ropshik ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da kula da iyalan marigayin tare da tuna gudunmawar da ya bayar ga ci gaban aikin jarida.

Marigayi Leo Keyen ya rasu ya bar matarsa guda ɗaya, ‘ya’ya huɗu da jikoki uku. Allah Ya jikansa da rahama. Ameen.

Ga Rahoton Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/07/AUD-20260704-WA0020.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Rumbun Hotuna

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani
Next Post: Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass

Karin Labarai Masu Alaka

Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango Afrika
Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya Labarai
Shari’ar Ta’addanci: Manyan Jagororin Ansaru Biyu Sun Amsa Laifi A Abuja Afrika
Netanyahu Yana Neman Shawarwari Daga Hukumomin Lebanon Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • Gwamna Ahmad Aliyu Na Jihar Sokoto Ya Gabatar Da Kasafin Fiye Da Naira Biliyan 700 Labarai
  • Shugaban Ƙasar China Zai Karbi Bakwancin Shugaban Koriya Ta Kudu Afrika
  • Gwamnatin Jihar Neja Ta Soke Lasisin Mallakar Wasu Manyan Filaye A Jihar Labarai
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
  • Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya Najeriya
  • Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.