Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass
Published: July 5, 2026 at 4:53 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tawagar masu yaɗa labarai da ke halartar shirin Arewa Media Summit ta kai ziyara zuwa aikin gina Kano Northern Bypass, a ci gaba da rangadin manyan ayyukan gwamnatin tarayya da ake aiwatarwa a Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rangadin ya gudana ne bisa jagorancin Ofishin Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Abdulaziz Abdulaziz, domin bai wa mahalarta taron damar ganin ci gaban ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a Arewacin Najeriya.

Aikin Kano Northern Bypass, mai tsawon kusan kilomita 38, ya taso daga hanyar Kano–Hadejia zuwa hanyar Kano–Katsina. Ana sa ran kammala aikin zai rage cunkoson manyan motoci da ke bi ta cikin birnin Kano tare da sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki da fasinjoji.

Masana sun bayyana cewa aikin zai rage asarar lokaci da kuɗaɗen sufuri, ya bunƙasa harkokin kasuwanci da masana’antu, tare da ƙara jawo masu zuba jari zuwa yankunan Zaura, Dawanau, Tarda da sauran al’ummomin da ke kewaye da hanyar.

Haka kuma, ana hasashen aikin zai samar da sabbin guraben ayyukan yi ga matasa da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihar da ma yankin Arewa baki ɗaya.

Masu shirya Arewa Media Summit sun ce rangadin na ba ‘yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta damar ganin ayyukan da ido, domin su samar wa al’umma sahihan rahotanni masu dogaro da hujjoji kan ci gaban da ake samu a ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ana sa ran taron Arewa Media Summit zai gudana ranar 6 ga Yulin 2026 a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnatin jihar Kano, inda zai haɗa manyan ‘yan jarida, masana, masu tasiri da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna rawar kafafen yaɗa labarai wajen bunƙasa ci gaban Arewa da Najeriya baki ɗaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen
Next Post: Gombe Da UNFPA Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Yaƙi Da Cutar Fistula Da Tamowa

Karin Labarai Masu Alaka

Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand Kimiya
Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
Jirgi Marar Matuki Yayi Ajalin A Kallah Mambobin M23 9 Tare Da Kashe Kakakin Rundunar Afrika
ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haifar Da Mutuwar Mutane A Nairobi Afrika
  • Gangamin Wayar Da Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Jihar Gombe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Damke Matasa Masu Gurza Kudaden Ketare Na Jabu Afrika
  • Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika
  • Afirka Ta Kudu Da Kenya Sun Bayyana Yaudarar ‘Yan Kasashe Da Yawa Tare Da Sakasu Yaki Labarai
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.