Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Afirka Ta Kudu Da Kenya Sun Bayyana Yaudarar ‘Yan Kasashe Da Yawa Tare Da Sakasu Yaki
Published: February 26, 2026 at 9:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Afrika ta kudu da Kenya a ranar Alhamis suke kara bayyana cewa ‘yan kasashen masu yawa ne aka yaudare su shiga yakin Rasha da Ukraine, domin hukumomi a Pretoria sun bada rahoton ‘yan kasar biyu sun mutu a fagen daga, yayinda wata kotu a Nairobi ta tuhumi wani mutum da laifin safarar ‘yan kasar 25 domin suyi yaki a bangaren Rasha a fafatawar da kasar take yi da Ukraine.

Afrika ta kudu ta fada cewa ‘yan kasar biyu da suka mutu a fagen yaki basa cikin ‘yan kasar su 17 da aka yaudara suka taya Rasha yaki a Ukraine, wadanda galibin su an ceto su sun koma kasar, kamar yadda wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ranar Alhamis. Ma’aikatar bata fadi lokaci da kuma yanayin da ya kai ga mutuwar mutanen biyu ba.

Hukumomin Rasha sun musanta cewa suna daukar ‘yan kasashen Afirka aikin soja ba bisa ka’ida ba domin yakinta da Ukraine.

“gwamnati tana ci gaba da binciken kungiyoyi da suke da hanu wajen daukar ‘yan kasa zuwa Rasha, da zummar hukunta dukkan wadanda suke da hanu ciki,” kamar yadda doka ta tanada, ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta kudun ta fada.

A Nairobi, kotu ta tuhumi wani dan kasar mai suna Festus Arasa Omwamba, darektan wani kamfanin samarwa mutane ayyyukan yi da laifin safarar mutane zuwa Rasha ta hanyoyin yaudara, kamar yadda ofishin Daraktan gabatar da kararraki na kasar ya fada.

Ma’aikatar shari’ar tace an ceto mutane 22 cikin 25, a wani daki a karamar hukumar Machakos da bashi da nisa da babban birnin kasar cikin watan Nuwamban bara. Uku daga cikin wannan adadi tuni suka sapmi kansu a fagen daga a Ukraine.

Fiye da ‘yan kasashen Afirka dubu daya da dari bakwai ne suke yaki a bangaren Rasha a fafatawar da kasar take yi da Ukraine.

Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi
Next Post: Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
Shugaba Donald Trump Ya Nada Shugaban Bankin Tarayya Amurka
Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
  • Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025, Wasanni
  • Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
  • Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
  • Haryanzu Abubakar Malami Da Dansa Suna Hannun Hukumar EFCC Labarai
  • Shugaban Kasar Tunisiya Ya Tsawaita Dokar Da Baci A Kasar Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.