Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika

Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio)
Published: December 5, 2025 at 8:38 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 5, 2025

Gwamna Inuwa Yahaya zai aiwatar da sabon tsarin bunƙasa Rigakafin cutar Polio a yan kunan Karkara tare da haɗin gwiwa da gidauniyar Gates.

A ranar Alhamis ne Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya karɓi baƙoncin wata tawaga daga Gidauniyar Gates, ƙarƙashin jagorancin Daraktar yaki da Cutar Polio ta duniya, Kathy Neuzil.

Taron wanda aka gudanar a masauƙin Gwamnan na Gombe dake Abuja, ya ta’allaƙa ne kan zurfafa haɗin gwiwa don inganta rigakafin cutar shan inna, musamman a yankunan dake fama da matsalar tsaro a Arewacin kasar.

Tattaunawar ta kuma lalubo matakan inganta tsaro, da haɗa kan al’umma da tsare tsaren sanya ido, tare da fayyace lokaci da matakan ƙara ƙaimi wajen ganin an kawar da Cutar shan Inna daga Najeriya.

A matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma shugaban Kwamitin Majalisar Tattalin Arzikin kasa kan kawar da cutar shan inna, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada ƙudurinsa na tallafawa ƙoƙarin da al’umma ke yi na kawar da cutar.

Ya yaba da muhimmiyar rawar da Gidauniyar Gates ta taka tare da jaddada buƙatar ci gaba da yin haɗin gwiwa, musamman a wuraren da rashin tsaro ke haifar da ƙalubale ga ayyukan rigakafi.

“Gaskiya ne cewa wasu jihohi suna fama da manyan ƙalubalen tsaro dake hana ma’aikatan rigakafi kaiwa ga wasu yankuna, amma a matsayina na shugaban kwamitin majalisar tattalin arziƙin kasa kan kawar da cutar shan inna, zan ci gaba da jan hankalin takwarorina da hukumomin tsaro dama wadanda abin ya shafa don ƙarfafa hanyoyin kaiwa ga irin waɗannan yankuna kuma idan akwai buƙatar matakan tsaro na musamman don kare ma’aikatan rigakafin, mun shirya tsaf don samar da hakan.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa tuni aka fara ɓullo da sabbin dabarun tsaro tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa waɗannan matakai za su inganta hanyoyin samun sauƙi da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatan dake sahun gaba a gangamin rigakafi.

Ya kuma baiwa gidauniyar tabbacin ci gaba da bada goyon bayansa wajen samar da haɗin kai a tsakanin gwamnonin Arewa don kyautata harkar rigakafi da kuma ɗorewar gangamin kawar da cutar.

Ya buga misali da “tsarin Gombe”, wanda aka gina bisa ƙwaƙƙwaran tsarin damawa da al’umma, tsarin da aka shimfiɗa bisa ingantacciyar manufa, a matsayin tsarin da za a iya ɗabbaƙawa a faɗin yankin don samun sakamako mai kyau.

A nata jawabin, Daraktar Gidauniyar ta GF Global Polio, Kathy Neuzil, ta bayyana damuwa kan yadda al’ummomi da dama ke fama da matsalar tsaro, ta kuma nemi haɗin kai da Gwamna Inuwa Yahaya, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma shugaban kwamitin yaƙi da cutar shan inna na Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa NEC, don haɗa kai da shugabanni a jihohi da hukumomin tsaro wajen samar da kariya ga ma’aikatan lafiyan dake gudanar da rigakafin cutar ta Polio.

Ta yabawa jagorancin Gwamnan da irin gagarumin ci gaban da aka samu a jihar Gombe, inda ta bayyana cewa masu bada tallafi suna sanya ido sosai saboda ganin jajircewar shugabanni, da yadda ake damawa da al’umma da kuma nasarorin da ake samu.

“Mun yaba da gagarumin ƙuduri da jajircewar da muka gani a Jihar Gombe,” in ji Neuzil.

Ta ƙara da cewa, “Yin aiki tare da gwamnatocin jihohi, musamman a ƙarƙashin jagorancinka a Kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa, yana ba mu ƙwarin gwiwar cewa za a iya cike giɓin da ake da shi.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya samu rakiyar kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Dr. Habu Ɗahiru da Sakataren Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta GoHealth, Dr. Abubakar Musa Yahaya da Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta jihar Gombe, Dr. Abdulrahman Shuaibu Jimeta.

Tawagar Gidauniyar ta Gates ta haɗa da Daraktar kawar da Cutar Polio ta Duniya Kathy Neuzil da Mataimakan Darakta Yusuf Yusufari da Andrew Stein.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba
Next Post: Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC

Karin Labarai Masu Alaka

Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa Afrika
Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
Azumin Ramadan Yahadu Da Azumin Lent Da Mabiya Addinin Kirista Sukeyi A Wannan Shekarar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • FIFA Na Shirin Fadada Babban Na’urar VAR A Gasar Cin Kofin Duniya 2026. Wasanni
  • Kungiyar Maharba Da ‘Yan Sintiri Sun Samu Kyautar Motoci Labarai
  • Sudan Takai Hari Kasar Chadi Da Jirgi Marar Matuki Afrika
  • An Shirya Taron Horas Da Matasa Gabanin Wasan Motsa Jiki 2025 Wasanni
  • Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Ya Roki Rasha Ta Taimakawa Kasar Afrika
  • Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.