Gwamnatin jihar Gombe ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar kula da mata masu fama da cutar yoyon fitsari sakamakon haihuwa (Obstetric Fistula) da kuma cibiyar kula da yara masu matsanancin tamowa a Babban Asibitin Deba, da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba.
Da yake ƙaddamar da cibiyoyin a madadin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamnan jihar Gombe, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya ce aikin ya nuna ƙudirin gwamnati na ci gaba da inganta harkokin kiwon lafiya da kare lafiyar al’umma.

Ya bayyana cewa tun bayan hawan gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya a shekarar 2019, an mayar da harkokin lafiya cikin manyan manufofin ci gaban jihar ta hanyar gina cibiyoyin lafiya masu aiki na sa’o’i 24 a dukkan gundumomi 114 na jihar, faɗaɗa kayayyakin more rayuwa na kiwon lafiya da kuma aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi lafiyar jama’a.
Dakta Jatau ya ce an gina da kuma tanadi cibiyar kula da masu cutar fistula ne da tallafin Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai Kula da Yawan Jama’a (UNFPA), sakamakon haɗin gwiwa da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Jihar Gombe.
A cewarsa, cibiyar za ta samar da cikakkiyar kulawa ga mata masu fama da cutar fistula domin dawo da lafiyarsu, mutuncinsu da kuma martabarsu a cikin al’umma, yayin da cibiyar kula da yara masu matsanancin tamowa za ta taimaka wajen rage mace-macen yara ta hanyar ba su kulawa ta musamman.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya, shugabannin al’umma da mazauna yankin da su tabbatar da kula da cibiyoyin yadda ya kamata domin su ci gaba da anfani ga al’umma. Haka kuma ya buƙaci jama’a su rungumi rigakafi da sauran matakan kariya daga cututtuka domin inganta lafiyar al’umma.
Tun da farko, Babban Sakataren Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Ali Jalo, ya ce ƙaddamar da cibiyoyin wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da kowa ya samu ingantacciyar kulawar lafiya, musamman mata, jarirai da yara.

Shi ma Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar Gombe, Idris Yambiyu Buba, ya yabawa abokan hulɗa na ci gaba bisa gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa harkokin lafiya a jihar, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da su.
A nasa jawabin, wakilin Hukumar UNFPA ya ce cibiyar za ta ƙara ƙarfafa yaƙi da cutar fistula a jihar, yana mai bayyana cewa Yamaltu Deba na daga cikin yankunan da ke da yawan masu fama da cutar. Ya ƙara da cewa mata 151 sun amfana da shirin kula da cutar a shekarar 2025 ta hanyar haɗin gwiwar Gwamnatin jihar Gombe da gwamnatin Norway ta hannun UNFPA.

Shi kuwa wanda ya kafa ƙungiyar Taimaka, Dakta Abubakar Umar, ya bayyana cewa cibiyar kula da yara masu tamowa tana da gadaje 203 tare da shirin faɗaɗa su zuwa 250. Ya ce cibiyar na da likitoci bakwai da ma’aikatan jinya sama da 50, kuma tana ba da magani kyauta ga duk yaran da ke buƙata.
Sarkin Deba, Alhaji QS Ahmed Usman, da Shugaban Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, Alhaji Yunusa Yakubu, sun yabawa gwamnatin jihar da abokan hulɗarta bisa samar da cibiyoyin, tare da kira ga iyaye su guji auren yara ƙanana, wanda suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cutar fistula.
An kammala bikin ƙaddamarwar da gabatar da shaidun wasu mata da suka warke daga cutar fistula, tare da miƙa kayan aikin jinya, magunguna da sauran kayayyakin kula da marasa lafiya ga cibiyoyin.



