Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz
Published: July 6, 2026 at 5:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci masu tasiri a kafafen sada zumunta da sauran masu yaɗa bayanai su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa, tana mai jaddada cewa yaɗa labaran ƙarya na iya haifar da rikice-rikice tare da barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Abdulaziz Abdulaziz, ne ya bayyana hakan a jawabin maraba da ya gabatar yayin buɗe taron farko na Arewa Media Summit, wanda aka gudanar a ranar Litinin a Kano.

Ya ce bunƙasar dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa na buƙatar amincewa da haɗin kai tsakanin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da kuma al’umma, yana mai cewa taron ya tattaro shugabanni, ‘yan jarida, masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, masu tasiri da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin ƙarfafa alaƙar gwamnati da jama’a ta hanyar gaskiya, riƙon amana da ɗabi’ar aikin jarida.

Abdulaziz ya bayyana cewa taken taron, “Government-Citizen Accord: Accountability, Responsibility and Ethical Media Practice,” ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sake gina amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.

A cewarsa, gwamnati na da alhakin samar da sahihan bayanai cikin buɗaɗɗen tsari, yayin da al’umma ke da nauyin tabbatar da gaskiyar bayanai kafin yaɗa su, tare da riƙe gwamnati da alhakin ayyukanta ta hanyar lumana da bin doka.

Ya ƙara da cewa kafafen yaɗa labarai su ne gada tsakanin gwamnati da jama’a, yana mai cewa ingantaccen aikin jarida da tabbatar da sahihancin labarai na taka muhimmiyar rawa wajen gina zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Ya jaddada cewa masu tasiri a shafukan sada zumunta sun zama manyan masu yaɗa bayanai a wannan zamani, don haka wajibi ne su riƙa tantance gaskiyar bayanai kafin wallafawa.

«”A yau, saƙon da aka wallafa na iya haifar da fata ko kuma tayar da husuma cikin ɗan lokaci. Don haka bai kamata neman farin jini ko yawan masu kallo ya zama sanadin jefa ƙasa cikin rikici ba,” in ji shi.»

Abdulaziz ya kuma yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta su taka rawar gani wajen kare zaman lafiyar ƙasa yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙaratowa, tare da gyara duk wani kuskure idan ya faru.

Ya bayyana cewa a wani ɓangare na shirye-shiryen taron, an horas da sama da mutum 100 daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dabarun yaɗa bayanai da kuma bayyana manufofi da nasarorin gwamnati yadda ya kamata.

Haka kuma, ya sanar da ƙaddamar da shirin Gani-Ya-Kori-Ji, wanda zai zagaya jihohin Arewacin Najeriya domin haska ayyukan ci gaba da Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka aiwatar, musamman waɗanda ba su samu isasshen haske daga kafafen yaɗa labarai ba.

A cewarsa, taron ya nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare ‘yancin faɗin albarkacin baki, ƙarfafa tattaunawa da bunƙasa dimokuraɗiyya.

Ya ce an tsara taron ne domin bai wa masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya damar tattaunawa kan yadda za a inganta alaƙar gwamnati da jama’a.

A ƙarshe, Abdulaziz ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa karɓar baƙuncin taron, yana mai bayyana Kano a matsayin cibiyar siyasa, kasuwanci da tattaunawa a Najeriya.

Ya kuma buƙaci mahalarta taron su fito da shawarwari da sabbin alƙawurra da za su inganta buɗaɗɗen tsarin mulki, ƙarfafa ɗabi’ar aikin jarida da kuma bunƙasa kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da al’umma.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gombe Da UNFPA Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Yaƙi Da Cutar Fistula Da Tamowa
Next Post: Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi

Karin Labarai Masu Alaka

Baital Malin Amurka Tace Sahannun Trump Zai Fito A Kudin Kasar Amurka
Hukumar NDLEA Ta Kama Wata Mata Da cikin Bogi Na ƙwaya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ga Alamu Jakuna Za Su Bace A Doron Kasa Nan Da Shekaru 5 Labarai
Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Najeriya
Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
Babban Bankin Najeriya Ya Rage Kudin Ruwa Da Kashi Daya Cikin Dari Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
  • Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
  • NYSC – Sai An Gabatar Da Takardar NERD Kafin Shiga Bautar Ƙasa Afrika
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali Najeriya
  • Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist
    Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo Wasanni
  • Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa Afrika
  • An Bukaci Mabiya Addinin Kirista Da Suyi Koyi Da Rayuwar Yesu Najeriya
  • Athletic Club Ta Doke Atlético Madrid 3-0, Julian Alvarez Ya Koma Wasa Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.