Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi
Published: July 6, 2026 at 6:35 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da haɗa baki wajen aikata laifi, yin barazanar garkuwa da mutum ta hanyar kira da saƙonnin waya ba tare da bayyana ainihin su ba, tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 30.

Mai magana da yawun rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani mazaunin garin Jega, Alhaji Aminu Garba, ya kai rahoton cewa yana karɓar kiraye-kirayen waya masu ɗauke da barazanar yin garkuwa da shi idan har bai biya Naira miliyan 30 ba.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Muhammad Shafiu mai shekaru 21, Mansur Ibrahim mai shekaru 21, Aliyu Umar mai shekaru 25 da kuma Muhammad Suleiman mai shekaru 23.

Binciken farko ya nuna cewa mutane uku daga cikin waɗanda ake zargin sun sayi sabon layin waya, sannan suka riƙa kiran wanda abin ya shafa, inda ɗaya daga cikinsu ya canja murya domin ta yi kama da ta Bafullatani, da nufin tsoratar da wanda ake yi wa barazanar tare da ɓoye ainihin sa.

Binciken ya kuma gano cewa Muhammad Suleiman, wanda ake zargin abokin iyalan wanda aka yi wa barazanar ne, ya bayar da lambar wayarsa da wasu bayanan iyalansa, waɗanda aka yi amfani da su wajen aiwatar da wannan shiri.

Rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar gano tare da cafke waɗanda ake zargin a ƙauyukan Gumbin Kure da Gamjeji da ke Ƙaramar Hukumar Maiyama, lamarin da ya dakile shirin kafin a aiwatar da shi.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya ba da umarnin zurfafa bincike tare da gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bisa tanadin doka.

Ya kuma jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu a laifukan garkuwa da mutane, karɓar kuɗin fansa ko makamantansu zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Rundunar ta buƙaci al’umma su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da kai rahoton duk wani kira ko motsi da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz
Next Post: Yobe Ta Sake Jaddada Ƙudirin Rage Mutuwar Yara

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
NDLEA Ta Fara Binciken Kwakwaf Akan Wasu ‘Yan Mata Dake Kai Kwaya Gidan Yari Labarai
An Gudanar da Taron Kwana Biyu kan Tsarin Sa Ido da Tantance Ayyukan AGILE a Jihar Gombe  Afrika
Shugaban Kasar Faransa Ya Zanta Da Shugaban Kasar Iran Afrika
Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
  • Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro Afrika
  • Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai Afrika
  • Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai Afrika
  • Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga Labarai
  • Mali Da Burkina Faso Za Su Haramta Wa Amurkawa Izinin Shiga Ƙasashen Su Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tinubu Ya Nada Shugabannin Hukumar NERC Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.