Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, tsohon Gwamnan farar hula na farko na tsohuwar Jihar Gongola, kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa.
Alhaji Bamanga Tukur ya rasu ne a ranar Asabar bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya fitar a ranar 12 ga Satumba, 2026, Gwamna Fintiri ya bayyana marigayin a matsayin babban ɗan ƙasa, hamshakin ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan siyasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.
Gwamna Fintiri ya ce rasuwar Alhaji Bamanga Tukur babban rashi ne ga Jihar Adamawa da Najeriya baki ɗaya, yana mai yaba wa marigayin bisa jajircewarsa, hangen nesa, kishin ƙasa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar da ƙasa.
Ya ce shi da kansa zai yi kewar shawarwari masu amfani da hikimar da marigayin ke bayarwa kan al’amuran jihar da ƙasa.
Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa, abokan hulɗarsa da al’ummar Jihar Adamawa, yana mai kira gare su da su samu ƙwarin gwiwa daga kyakkyawan tarihin hidima da jagorancin da ya bari.
A matsayin girmamawa ga marigayin da kuma karrama irin gudunmawar da ya bayar, Gwamna Fintiri ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a fadin Jihar Adamawa.
A yayin zaman makokin, za a sauke tutocin gwamnatin jihar zuwa rabin sandar tuta.
Gwamna Fintiri ya kuma roƙi Allah Ya gafarta wa Alhaji Bamanga Tukur kura-kuransa, Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa, tare da bai wa iyalansa da sauran waɗanda rasuwar ta shafa ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.


