Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

ACReSAL Ta Tallafa Wa FMC Kumo, Ta Shuka Bishiyoyi Tare Da Gyara Magudanan Ruwa
Published: September 4, 2026 at 12:48 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL), ta hannun Jewel Environmental Initiative (JEI), ya gudanar da ayyukan kare muhalli da tallafawa harkokin kiwon lafiya a Asibitin Federal Medical Centre (FMC), Kumo, a jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya

Ayyukan sun hada da shuka bishiyoyi, gyaran da cire laka daga magudanan ruwa, da kuma bai wa asibitin kayan amfani na kiwon lafiya, da nufin inganta tsaftar muhalli, rage tara ruwa da kuma samar da yanayi mai kyau da aminci ga marasa lafiya, ma’aikata da sauran masu ziyartar asibitin.

Da yake wakiltar Daraktan Kiwon Lafiya na FMC Kumo, Daraktan Ayyukan Jinya da Horarwa na asibitin, Dr. Nuhu Ardo Kumo, ne ya kaddamar da aikin shuka bishiyoyin, inda ya shuka bishiya ta farko. Ya samu rakiyar Shugaban Sashen Jinya, Alhaji Abdulkadir Bala Minjibir.

A yayin aikin, JEI ta kuma gudanar da aikin cire laka da tarkace daga magudanan ruwa da ke cikin harabar asibitin, lamarin da zai taimaka wajen inganta zirga-zirgar ruwa, rage hadarin tsayawar ruwa da kuma kara tsaftar muhalli.

Haka kuma, ACReSAL ta hannun JEI ta bai wa FMC Kumo kayan amfani na asibiti, ciki har da safunan tiyata (surgical gloves), domin tallafawa ayyukan kiwon lafiya da asibitin ke gudanarwa.

Da yake magana a madadin Daraktan Asibitin, Dr. Nuhu Ardo Kumo ya yabawa ACReSAL da JEI bisa wannan tallafi, yana mai cewa shuka bishiyoyi da gyaran magudanan ruwa za su taimaka wajen samar da muhalli mai tsafta, lafiya da aminci ga marasa lafiya da ma’aikatan asibitin.

Shi ma Jami’in Sa-ido da Tantance Ayyuka na JEI, Mal. Dahiru Adamu, wanda ya yi magana a madadin Babban Daraktan JEI, Alhaji Samaila Bima, ya gode wa mahukuntan FMC Kumo bisa kyakkyawar tarba da hadin kai da suka bayar wajen gudanar da aikin.

Ya kuma yaba wa jagorancin Daraktan Kiwon Lafiya na farko na asibitin, Dr. Mu’azu Shu’aibu Ishaq, bisa ci gaban da aka samu a cibiyar, tare da jaddada cewa JEI za ta ci gaba da tallafawa asibitin da ayyukan da za su inganta muhalli.

A cewarsa, irin wadannan ayyuka na cikin kokarin JEI na bayar da gudunmawa wajen cimma manufofin Majalisar Dinkin Duniya na Sustainable Development Goals (SDGs), musamman wadanda suka shafi lafiya da walwalar jama’a, tsaftataccen ruwa da muhalli, al’ummomi masu dorewa, yaki da sauyin yanayi da kare muhalli.

Aikin ya kuma nuna muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula da cibiyoyin kiwon lafiya wajen kare muhalli, yaki da illolin sauyin yanayi da kuma inganta rayuwar al’umma.

Afrika, Kimiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Hadakar Kungiyoyin Sauyin Yanayi Ta Bukaci ‘Yan Siyasa Su Dauki Matakan Kare Muhalli
Next Post: NEDC Ta Karyata Bada Tallafin Karatun MSc Da Ke Yawo A Kafafen Sadarwa

Karin Labarai Masu Alaka

Farashin Danyen Mai Ya Farfado Fiye Da Kashi Daya Sauran Duniya
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai
‘Yan Sandan Gombe Sun Yi Taron Gaggawa Da Jam’iyyun Siyasa Da INEC Kan Tsaro Labarai
Ferfesa Pantami Yayi Watsi Da Amincewa Da Jamilu Isiyaku Gwamna Afrika
An Tsinto Gawarwakin ‘Yan gudun Hijira A Bakin Tekun Comoros Labarai
Makarantun Allo Zasu Yi Gogayya Da Na Boko Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Real Madrid Ta Sauya Tsarin Gabatar Da Mourinho Da Sabbin ’Yan Wasanta A Santiago Bernabéu Wasanni
  • Hotunan Hawan Sallah A Masarautar Bauchi Afrika
  • Bahagon Mancha Ya Buge Bahagon Maitakwasara Da Wasun Su! Nishadi
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya Labarai
  • Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
  • Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.