Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8
Published: August 31, 2026 at 3:38 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Bauchi a Arewa Maso Gabashin Najeriya ta kama wani dattijo mai shekaru 70, Usman Abubakar, bisa zargin lalata da wata yarinya ’yar shekara takwas a yankin Tsakanin Bayara da ke cikin birnin Bauchi.

Mahaifin yarinyar, mai shekaru 48, ne ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na ‘E’ Division da ke Yelwa.

Ya zargi Abubakar, wanda ke zaune a yankin, da jan hankalin ’yarsa zuwa wani ginin da ba a kammala ba a ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta, inda ake zargin ya yi lalata da ita.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya bayyana cewa kama wanda ake zargin na daga cikin kokarin rundunar na dakile cin zarafin mata da yara da kuma sauran nau’o’in tashin hankali bisa jinsi.

Ya ce bayan samun rahoton, jami’an ’yan sandan sun gaggauta daukar mataki tare da cafke wanda ake zargin.

SP Habib ya ce yayin gudanar da tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin.

An garzaya da yarinyar zuwa asibitin ’yan sanda domin duba lafiyarta da kuma ba ta kulawar da ta dace.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da lamarin, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam
Next Post: RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH

Karin Labarai Masu Alaka

An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
2025 Ta Bar Baya Da Abubuwa Masu Ban Al’ajabi, 2026 Barka Da Zuwa! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Rashin Kyawun Hanyoyi Babbar Matsalace A Najeriya Afrika
Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe Afrika
TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi Afrika
  • Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku Labarai
  • Kamaru Ta Lallasa Malawi 3-0, Ta Lashe Kofin WAFCON Na Farko A Tarihi Wasanni
  • Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka Labarai
  • An Samar Da Dala Kusan Biliyan Biyu Don Yakar Polio Labarai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk. Wasanni
  • An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa Afrika
  • Ana Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Trump Da Zelensky Domin Tsagaita Wuta A Ukraine Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.