Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a Karkara ta jihar Gombe, Dake Arewa Maso Gabashin Najeriya wato RUWASSA, ta shirya taron masu ruwa da tsaki domin tantancewa da tabbatar da ingancin wasu muhimman tsare-tsare uku da hukumar ta samar a ƙarƙashin shirin NG-SURWASH.
An gudanar da taron ne domin bai wa masu ruwa da tsaki damar nazarin takardun tsare-tsaren, gabatar da shawarwari da gyare-gyare, tare da tabbatar da cewa za a iya amfani da su a matsayin muhimman takardun jagora wajen aiwatar da shirin, musamman a fannin inganta ƙwarewar ma’aikata da ƙarfafa hukumomi.
Da yake buɗe taron, Babban Manajan RUWASSA, Injiniya Mohammed Gibrimu Ahmed, ya yaba wa masu ruwa da tsakin bisa ci gaba da goyon baya da jajircewa wajen aiwatar da ayyukan shirin NG-SURWASH a jihar.
Injiniya Gibrimu ya buƙaci mahalarta taron da su mai da hankali sosai tare da shiga cikin tattaunawar da aka shirya yi kan tsare-tsaren uku.
Ya ce halartar tattaunawar yadda ya kamata zai bai wa mahalarta damar fahimtar takardun, gabatar da abubuwan da suke ganin ya kamata a gyara, da kuma neman ƙarin bayani kan batutuwan da ba su fahimta sosai ba.
Babban Manajan ya bayyana cewa, bayan an yi la’akari da shawarwari da gudunmawar masu ruwa da tsaki, tsare-tsaren za su zama ingantattun takardun aiki da za a dogara da su wajen aiwatar da shirin.
Ya bayyana cewa tsare-tsaren ukun sun haɗa da Ka’idar Ayyukan Gudanarwa (Standard Operating Procedure – SOP), Tsarin Gudanar da Albarkatun Ma’aikata (Human Resource Management Plan), da Tsarin Gudanar da Ayyuka da Kulawa (Operations and Maintenance Plan).
Ya ce tsare-tsaren na da nufin ƙarfafa ƙwarewar hukumomi da masu ruwa da tsaki, tare da inganta yadda ake aiwatar da shirin NG-SURWASH yadda ya kamata.
Shi ma da yake jawabi, Mai Gudanar da Shirin NG-SURWASH na Sashen Kula da Ayyukan Shirin na Jihar Gombe, SPCU, Injiniya Usman Abubakar Aliyu, ya taya mahalarta murna, tare da kira gare su da su ƙara jajircewa wajen fahimtar dukkan sassan shirin da sauran muhimman abubuwan da suka shafi aiwatar da shi.
Ya ce fahimtar shirin da kuma bayar da gudunmawar masu ruwa da tsaki na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da an cimma manufofin shirin tare da samar da sakamakon da ake sa ran samu.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Gombe, GOSEPA, Dakta Auwalu Baba Jada, ya yi maraba da mahalarta taron, tare da ƙarfafa gwiwar hukumomin da ke aiwatar da shirin da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da aiki tare.
Dakta Jada ya ce haɗin gwiwa tsakanin hukumomin zai taimaka wajen samar da sakamako mai ɗorewa da inganci, yana mai cewa dukkan hukumomin da ke aiwatar da shirin suna taimaka wa juna wajen cimma manufofin shirin.
Ya kuma yaba wa Mai Gudanar da Shirin NG-SURWASH bisa ci gaba da bayar da goyon baya da shawarwari ga hukumomin da ke aiwatar da shirin.
Mahalarta taron sun haɗa da ma’aikatan RUWASSA, masu kula da harkokin WASH a ƙananan hukumomi, jami’an sa ido da tantance ayyuka daga ƙananan hukumomin Akko, Balanga, Dukku, Kwami, Kaltungo, Shongom, Nafada da Yamaltu Deba, da kuma mambobin Kwamitocin Ruwa, Tsafta da Kiwon Lafiya, WASHCOMs, daga ƙananan hukumomin da aka gayyata.
Hukumar ta gayyato ƙwararrun masana domin jagorantar mahalarta wajen nazarin tsare-tsaren uku da kuma ƙara musu fahimta kan abubuwan da ke cikin takardun da yadda za a yi amfani da su.
Mataimakin Fasaha kan Kare Haƙƙin Al’umma a SPCU, Mataimakin Farfesa Adamu Jibir, ya gabatar da jawabi kan manufofin taron, abubuwan da ake sa ran cimmawa da kuma tsarin gudanar da taron.
Dakta Lukman Shiji Sadiq ya gabatar da bayani kan Ka’idar Ayyukan Gudanarwa (SOP), yayin da Dakta Musa Abdu daga Jami’ar Jihar Gombe ya gabatar da Tsarin Gudanar da Albarkatun Ma’aikata da RUWASSA ta samar.
Shi kuma Dakta Abubakar Umar Yuguda, Mataimakin Fasaha kan Kare Muhalli kuma ƙwararren masani kan muhalli, ya gabatar da Tsarin Gudanar da Ayyuka da Kulawa.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka yi jawabi sun yaba wa RUWASSA da shirin NG-SURWASH bisa shirya wannan muhimmin taro.
Sun yi alkawarin bayar da cikakkiyar gudunmawarsu wajen nazari da tantance tsare-tsaren ukun, suna mai cewa takardun za su taimaka matuƙa wajen ƙarfafa hukumomi, inganta aiwatar da shirin da kuma tabbatar da ɗorewarsa.
Daga cikin abubuwan da suka gudana a taron akwai zaman tattaunawa da musayar ra’ayi, gabatar da shawarwari da tsokaci kan tsare-tsaren ukun, da kuma ɗaukar hoton haɗin gwiwa.


