Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi
Published: September 1, 2026 at 8:00 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’yan sandan jihar Kogi a Najeriya ta sanar da ceto wasu ’yan bautar ƙasa wato NYSC 10, da aka yi garkuwa da su a jihar.

’Yan bautar ƙasar na cikin waɗanda wasu ’yan bindiga suka sace a ranar Laraba, 26 ga watan Agusta, a kan hanyar Aloma-Egane, da ke Ƙaramar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi.

Rahotanni sun ce ’yan NYSC ɗin na kan hanyarsu ne daga sansanin horas da matasa da ke Ƙaramar Hukumar Kolokuma/Opokuma a kihar Bayelsa, zuwa Abuja, bayan kammala shirinsu na horaswa.

Rundunar ’yan sandan ta ce maharan sun fito daga cikin daji ne a kusa da mahadar Ogene Zaria da Onicha-Igo, inda suka tare wasu motocin bas guda biyu tare da yin garkuwa da wasu daga cikin fasinjojin.

Bayan samun kiran neman agaji, jami’an tsaro sun isa wurin inda suka gano motocin bas ɗin da aka bari a wurin, sannan suka fara aikin bincike da tsefe dazuzzukan da ke yankin domin gano waɗanda aka yi garkuwa da su.

Tun da farko, rundunar ta sanar da ceto mutane 11, ciki har da direbobin motocin bas ɗin guda biyu, inda ta ce mafi yawansu ’yan NYSC ne.

A wani sabon aikin ceto kuma, rundunar ta ce an ƙara ceto wasu ’yan bautar ƙasa 10 ta hanyar haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda, sojoji da Hukumar DSS.

Rundunar ta bayyana aikin ceto a matsayin wanda aka gudanar cikin haɗin gwiwa tare da amfani da bayanan sirri, domin tabbatar da tsaron waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma tarwatsa ayyukan masu aikata laifin.

Rundunar ta ce aikin bincike da ceto sauran waɗanda ake zargin har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane yana ci gaba, tare da kokarin gano tare da cafke waɗanda suka aikata laifin.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kogi ya yaba wa jami’an ’yan sanda, sojoji, DSS da sauran jami’an tsaro da suka shiga aikin, bisa jajircewa da ƙwarewar da suka nuna wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ya kuma gode wa al’ummar yankunan da abin ya shafa bisa haɗin kai da kuma samar da bayanan sirri da ke taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

Rundunar ta ƙara kira ga jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da kai rahoton duk wani mutum ko motsi da suke zargi ga jami’an tsaro mafi kusa, domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro a yankin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha
Next Post: SCSN Ta Yi Kira Ga Hukumomi Su Tabbatar Da Bin Doka A shari’ar El-Rufa’i

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Namibiya Tayi Watsi Da Yarjejeniya Tsakanin Ta Da Kamfanin Total Labarai
Afirka Ta Kudu Ta Kubutar Da ‘Yan Kasar Da Suke Taya Sojojin Rasha Yaki Afrika
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka
Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika
Magajin Garin Istanbul Dake Kurkuku Ya Bukaci A Gudanar Da Zabe Labarai
Gwamna Zulum: Ya Bukaci Sojoji Su Cigaba Da Yakar Boko Haram Da ISWAP Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
  • Amurka Tayi Barazanar Rage Tallafinta Wa Sudan Ta Kudu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Fafaroma Leo Yayi Allah Wadai Bisa Karuwar Yake Yaken Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa Afrika
  • Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
  • An Zargi Shugaba Trump Da Kalaman Da Basu Dace Ba Afrika
  • Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
  • Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.