Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha Afrika
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH Afrika
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8 Afrika
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam Afrika

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jaddada Haƙuri Da Fahimtar Juna A Siyasa
Published: August 30, 2026 at 2:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu haƙuri, haɗin kai da zaman lafiya a harkokin shugabanci da siyasa.

Gwamnan ya kuma bukaci jama’a da su guji ƙiyayya, kalaman rarrabuwar kai da duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.

Inuwa Yahaya ya yi wannan kiran ne a wajen rufe gasar haddar Alƙur’ani da karatunsa karo na 29, wadda Ƙungiyar Izala Assasawar Sheikh Ismaila Idris Jos ta shirya a garin Bambam, ƙaramar hukumar ci gaban Balanga ta Kudu a Jihar Gombe.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya wakilci gwamnan a wajen taron.

Gwamna Yahaya ya yaba wa ƙungiyar bisa kokarin da take yi wajen tarbiyyantar da matasa ta fuskar addini da kuma bunƙasa karatun Alƙur’ani.

Ya tabbatar wa masu shirya gasar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta ɗabi’u da tarbiyya, tare da samar da al’umma masu tsoron Allah da sanin nauyin da ke kansu.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan al’umma ga gwamnatinsa, yana mai cewa nasarorin da Jihar Gombe ta samu a shekarun baya sun samu ne sakamakon haɗin kai da goyon bayan jama’a.

Ya yi kira ga al’umma da su kasance masu natsuwa, tare da guje wa kalamai ko ayyukan da za su iya haddasa tashin hankali, kawo rabuwar kai ko barazana ga zaman lafiyar jihar.

Ya ce haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da ɗorewar ci gaban Jihar Gombe.

Gwamnan ya ƙara da cewa nasarorin da jihar ta samu sun jawo hankalin wasu jihohi, waɗanda ke ƙara nuna sha’awa ga tsarin ayyukan raya ƙasa da Gombe ta fara aiwatarwa.

Tun da farko, Shugaban Majalisar Ulama ta Ƙungiyar Izala, Sheikh Hamza Abdulhamid, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da yi wa shugabanninsu addu’a tare da nuna haƙuri da juriya.

Malamin ya ce ƙungiyar Izala ta daɗe tana taka rawa wajen ilmantar da Musulmi, inda ta kafa makarantu a matakai daban-daban, tare da shirin kafa jami’a domin ci gaba da bunƙasa ilimin addini da na zamani.

Sheikh Hamza ya kuma yi gargadi kan kalaman rarrabuwar kai da rikice-rikicen da ba su da amfani, yana mai cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama sanadin ƙiyayya ko gaba tsakanin ‘yan kasa ba.

Ya bukaci jama’a da su rungumi tattaunawa, haƙuri da zaman lafiya, yana mai cewa siyasa ya kamata ta zama hanyar warware bambance-bambance, ba kuma hanyar haifar da rikici ba.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Bauchi Ya Shiga Neman Mafita Kan Lalacewar Matatar Ruwan Alkaleri
Next Post: Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi
  • Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
  • Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya Sauran Duniya
  • Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
  • PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
  • Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
  • Jagoran Adawar Uganda Bobi Wine Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.