Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo
Published: July 12, 2026 at 8:14 PM | By: Bala Hassan

Sakataren Polo na Bauchi a tarayyar Najeriya ya Jinjinawa Gwamna Bauchi Bala Mohammed saboda Inganta hanyar shiga filin Wasa da dakin baki da yayi.

Yayin da ake shirin fara gasar wasan Polo a Jihar Bauchi ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2026, Sakataren Kungiyar Polo ta Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Ningi, ya bayyana godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, Kauran Bauchi, bisa irin gudummawar da ya bayar wajen inganta filin wasan Polo.

Ningi” ya ce gwamnatin Bauchi karkashin Bala Mohammed ta aiwatar da muhimman ayyuka a filin wasan, ciki har da gyaran da inganta ɗakin baƙi da kuma sabunta hanyar shiga filin wasan, lamarin da ya ƙara wa filin kima tare da sauƙaƙa zirga-zirgar ga mahalarta gasar.

” Ya bayyana cewa waɗannan ayyuka sun nuna yadda gwamnatin jihar ke ba da muhimmanci ga bunƙasa harkokin wasanni da samar da ingantattun wuraren gudanar da su a fadin jihar

Sakataren ya ƙara da cewa wannan tallafi ya ɗaukaka martabar Kungiyar Polo ta Bauchi, tare da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan wasa, baƙi da sauran masu sha’awar wasan Polo da za su halarci gasar.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya saka wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed da alheri, tare da fatan gasar Polo ta bana za ta gudana cikin nasara da lumana.

Ya kuma yi kira ga dukkanin masy sha’awar wasan Polo da su bada hadin kai yayin da wasar ke guda na a jihar Bauchi da ke tarayyar Najeriya.

Manyan yan wasan Polo ne daga sassa daban -daban daga Najeriya harma da ƙasashen waje zasu halarci wannan gasar wacce za’a shafe kwanaki takwas ana fafatawa.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno
Next Post: Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi

Karin Labarai Masu Alaka

Janet Ce Gwarzuwar ‘Yar Wasan Mako NWFL Wasanni
Bassirou: Tawagar Senegal Zasu Samu Kyautar Kudi Da Filaye Sakamakon Nasarar Da sukayi AFCON 2025 Wasanni
Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot. Wasanni
Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
Barcelona na hangen Enrique Ko Arteta Wasanni
Alhassan Yayi Nasarar Kifar Da Wurkilili A Gasar Damben Gargajiya Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Amurka Donald Trump Ya Jadda da Kudirinsa Da Kwace Iyakar Greenland Amurka
  • Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha Afrika
  • Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru Afrika
  • Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
  • An Watse A Tattaunawar Tsakanin Rasha Da Ukraine Batare Da Cimma Matsaya Ba Labarai
  • Shirin Ga Fili GA Doki Shirye-Shirye
  • Wasu Muhimman Abubuwa Da Najeriya Ba Zata Manta Da Su Ba A 2025 Labarai
  • Barcelona Ta Lashe Kofin Spanish Super Cup  Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.