NSC Ta Bai Wa Shugabannin NFF Sa’o’i 24 Su Yi Murabus
Hukumar Kula da Wasanni ta Kasa (NSC) ta bai wa shugabannin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) wa’adin sa’o’i 24 da su yi murabus daga mukamansu, kamar yadda rahoton Arise News ya bayyana.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake kara samun matsaloli da cece-kuce kan yadda ake tafiyar da harkokin kwallon kafar Najeriya, da kuma yadda kungiyoyin kasar ke taka rawar gani a gasannin kasa da kasa.
Idan rahoton ya tabbata, wa’adin na iya kara tsananta rikicin da ya dade yana kunno kai tsakanin NSC da shugabannin NFF karkashin jagorancin shugaban hukumar, Ibrahim Gusau.
Super Eagles ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026, yayin da Super Falcons ma ta fuskanci babban koma baya bayan rashin samun tikitin kai tsaye zuwa gasar cin kofin duniya ta mata ta 2027.
Haka kuma, shugabancin NFF na fuskantar zarge-zargen rashin ingantaccen gudanarwa, almundahana da kuma wasu matakan da ake ganin sun taimaka wajen jefa kwallon kafar kasar cikin matsala.
Rahoton ya kuma zo ne yayin da ake kara samun kiraye-kirayen neman a yi cikakken garambawul a tsarin gudanar da kwallon kafar Najeriya tare da kara tabbatar da gaskiya da rikon amana.
A halin yanzu, ana jiran karin bayani kan matakin da NSC za ta dauka bayan cikar wa’adin sa’o’i 24, da kuma martanin shugabannin NFF kan wannan rahoto.


