Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Galatasaray Ta Yi Watsi Da Tayin €150m Daga Al-Hilal Kan Victor Osimhen
Published: August 20, 2026 at 5:41 PM | By: Bala Hassan

Galatasaray Ta Yi Watsi da Tayin €150m Daga Al-Hilal Kan Victor Osimhen

Kungiyar Galatasaray ta Turkiyya ta yi watsi da tayin da ya kai Yuro miliyan 150 daga Al-Hilal ta Saudiyya domin daukar dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen.

A cewar rahoton BSN Sports, Al-Hilal ta nuna sha’awarta ta daukar Osimhen, wanda Galatasaray ta dauka daga Napoli a farkon kakar wasan da ta gabata.

Rahoton ya ce tawagar Saudiyya karkashin jagorancin Yarima Nawaf bin Saad ta fara da tayin baki na Yuro miliyan 130, inda yariman ya sanar da shugabannin Galatasaray cewa zai zo Istanbul da kansa idan tattaunawar ta zama ta hukuma.

Bayan haka, Al-Hilal ta yi wa Osimhen tayin albashin Yuro miliyan 50 a duk shekara, amma Galatasaray ta sanar da kungiyar Saudiyyar cewa ba ta da niyyar sayar da dan wasan.

Daga bisani Al-Hilal ta kara tayin zuwa Yuro miliyan 150, amma har yanzu shugaban Galatasaray, Dursun Özbek, da shugabannin kungiyar sun yi fatali da tayin, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da rike dan wasan.

Osimhen, wanda rahoton ya ce yana matukar farin ciki a Galatasaray, ya kuma bayyana cewa abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne kakar wasa ta gaba, ba batun kudi ba.

Dan wasan na Najeriya ya kuma fara kakar gasar lig din Turkiyya da kyau, bayan ya zura kwallaye biyu a wasan makon farko da Çorum FK.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: NSC Ta Bai Wa Shugabannin NFF Sa’o’i 24 Su Yi Murabus
Next Post: Gombe Ta Yi Fice A Duniya: Maryam Dan’azumi Ta Lashe Gasar Alƙur’ani Na Ƙasa Da Ƙasa

Karin Labarai Masu Alaka

Chukwueze, Ya Ci Gaba Da Riƙe Rigarsa Mai Lamba 21 A AC Milan Wasanni
Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
FIFA, Ta Tabbatar Da Ranar Mika Sunayen ‘Yan Wasa AFCON 2025. Wasanni
Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
Nwakali Na Dab Da Komawa Kungiyar PAC Omonia Ta Cyprus Wasanni
Sabon Jadawalin Gasar Kwalon Kafa Ta Turai 2026 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
  • Messi Da Cristiano Suna Da Tasiri A Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Wasanni
  • Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen Afrika
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.