Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP
Published: January 24, 2026 at 5:34 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada tsayuwar sa kan akidun sa na siyasa, yana mai cewa ba zai sayar da ƙa’idojinsa domin amfanin kansa ba.

Kwankwaso ya bayana hakan ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da wasu shugabannin ƙananan hukumomi, wasu ’yan Majalisar Wakilai da wasu mataimaka, sun fice daga jam’iyyar NNPP.

Da yake jawabi ga magoya baya a gidan sa da ke Kano jim kaɗan bayan murabus ɗin gwamnan a ranar Juma’a, Kwankwaso ya ce gwagwarmayar sa ta siyasa tun farko ta ta’allaka ne kan ’yantar da talakawan Najeriya.

“Ni ba na sayarwa ba ne. Akidun siyasar mu ne ke tsayar da ni a kan hanya. Da ace neman riba ta kaina nake yi, da tuni na bi hanya mai sauƙi, kuma da ba ku same ni a nan ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ta tsaya tsayin daka ne bisa ɗabi’u da manufofi na bai ɗaya, ba wai saboda abin duniya ba.

“Manufa da hangen nesan mu ne ke ƙarfafa ni. Da ace kwaɗayi ne ke motsa ni, da tuni na karɓi kuɗi na gudu, kuma da ba ku zo nan nuna goyon baya ba,” ya ƙara da cewa.

Kwankwaso ya kuma buƙaci magoya bayan sa da su fara shiri da wuri gabanin zaɓukan gama-gari na 2027, yana mai gargaɗi kada a yi sakaci.

“Muna buƙatar mutane irin ku da suka sadaukar kuma suka tsaya kan gaskiya. Kada ku yi kasa a gwiwa, domin wata rana za mu cimma burinmu,” in ji shi.

Da yake magana kan abubuwan da ke faruwa a Kano a baya-bayan nan, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya jaddada muhimmancin fara shirye-shirye tun yanzu.

“Duba da abin da ke faruwa a Kano a yau, dole ne mu fara shiri, domin akwai mutanen da suka kuduri aniyar rusa abin da muka gina tsawon lokaci,” in ji shi.

“Manufa ta ita ce yaƙi don kare talakawa a kowane lokaci. Ba zan yi sulhu da masu cin zarafin jama’a ba,” in ji shi.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida
Next Post: Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika
Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa Labarai
Gwamnatin Sojan Burkina Faso Ta Soke Jam’iyyun Siyasar Kasar Afrika
Gwamna Inuwa Yahaya ya Rusa Majalisar Zantaswa ta Jihar Gombe Labarai
Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
  • Trump: Zamu Kawo Zaman Lafiya A Fadin Duniya Amurka
  • Yakin Rasha Da Ukrain Babban Kalubale Ne Ga Kasashen Turai Labarai
  • Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba Afrika
  • Kudi Sunfi Rayuwar Mutum Muhimmanci A Asibitocin Najeriya Kiwon Lafiya
  • Amurkawa Suna Turuwa Zuwa Kasar Faransa Duk Da Rashin Jituwa A Tsakanin Kasashen Amurka
  • Pakistan Da Afghanistan Sun Shiga Kwana Na Biyar Suna Fafatawa Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.