Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Kauran Gwandu Zai Inganta Wutan Lantarki A Kebbi
Published: January 5, 2026 at 11:25 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya amince da fitar da naira miliyan 650 domin sayewa da girke na’urar wutar lantarki mai karfin 15MVA, da nufin inganta samar da lantarki a fadin jihar.

Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

A cewar sa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta sakamakon rashin tabbataccen wutar lantarki.

Ya kara da cewa duk da cewa rarraba wutar lantarki hakki ne na Kamfanin KAEDCO, gwamnatin jihar ta ga dacewar shiga tsakani domin kare muradun jama’a.

Alhaji Tafida ya kuma bayyana cewa baya ga wannan kudin, gwamnatin Kebbi tana bada tallafin naira miliyan 150 duk wata ga KAEDCO, domin inganta ayyuka da tabbatar da dorewar wutar lantarki a jihar.

Ya yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai ta hanyar biyan kudin wutar lantarki akan lokaci, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka matuka wajen dorewar ingantaccen wuta a jihar.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na
Next Post: Manchester United Ta Sallami Ruben Amorim

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Zai Shafe Makonni Uku A Hutun Shekara-Shekara Afrika
APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika
Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
Iran Tace Jakadan Kasar Ta A Lebanon Zai Cigaba Da Zama A Beirut Afrika
Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Djibouti Yau Juma’a Afrika
Majalisar Dokokin Kamaru Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Sojan Burkina Faso Ta Soke Jam’iyyun Siyasar Kasar Afrika
  • Wani Abu Ya Fashe A Ofishin Jakadancin Amurka Dake Kasar Norway Afrika
  • Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Yayi Ajalin ‘Yan Ghana 50 Afrika
  • Patrick Vieira Ya Cimma Yarjejeniyar Zama Sabon Kocin Senegal Wasanni
  • Dakarun Sakai A Kasar Sudan Sun Kashe Mutane 28 A Wani Farmaki Afrika
  • Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump Amurka
  • Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami Tsaro
  • Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakai Don Farfaɗo Da Maɗaba’ar Gwamnati Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.