Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a
Published: June 29, 2026 at 4:02 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi goma sha ɗaya da kuma na sabbin Ƙananan Hukumomin Raya Karkara (LCDAs) da aka kafa a jihar, inda ya buƙace su da su tabbatar da amincewar da aka nuna musu ta hanyar jagoranci na gari da kuma inganta ayyukan yi wa al’umma hidima.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a Sabon Banquet Hall da ke Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, inda Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Musamman da Siyasa, Alhaji Salihu Adamu Sambo, ya jagoranci karɓar rantsuwar biyayya daga sabbin shugabannin.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsarwar, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana zaɓen ƙananan hukumomin da aka kammala kwanan nan a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana, adalci da gaskiya. Ya ce sakamakon zaɓen ya nuna irin amincewa da goyon bayan da al’ummar jihar ke bai wa gwamnatinsa da kuma jam’iyyar APC.

Gwamnan ya jaddada cewa ƙananan hukumomi su ne matakin gwamnati mafi kusa da jama’a, yana mai cewa kafa Ƙananan Hukumomin Raya Karkara (LCDAs) an yi ne domin ƙara kusantar da ayyukan gwamnati ga al’umma, inganta ayyukan ci gaba da kuma hanzarta bunƙasar yankunan karkara.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce lokacin da ya hau mulki a shekarar 2019 ya tarar da ƙananan hukumomin jihar cikin matsanancin ƙalubalen kuɗi, amma ta hanyar kyakkyawan tsari da kulawa wajen tafiyar da harkokin kuɗi, gwamnatinsa ta samu nasarar dawo da martabar su da daidaita harkokin kuɗaɗensu.

Ya kuma bayyana Hukumar Haɗin Gwiwar Ayyukan Raya Ƙasa (Joint Projects Development Agency) a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin gwamnatinsa, yana mai cewa hukumar ta samar da kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban.

Gwamnan ya hori sabbin shugabannin da aka rantsar da su da su gudanar da mulkinsu cikin riƙon amana, gaskiya, adalci da tsoron Allah, tare da gina kan nasarorin da waɗanda suka gabace su suka samar.

Haka kuma ya ƙalubalanci shugabannin da su tabbatar da cewa ayyukan da za su gudanar a mulki su zama hujjar da za ta ƙara jawo wa jam’iyyar APC goyon baya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, ya yi maraba da mahalarta taron, tare da yabawa al’ummar jihar kan yadda suka fito ƙwansu da kwarkwatarsu domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomi, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar jajircewarsu wajen ƙarfafa dimokraɗiyya.

Da yake jawabi a madadin sabbin shugabannin da aka rantsar, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Farfesa Abdullahi Bappah Garkuwa, ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da al’ummar jihar bisa amincewar da suka nuna musu, tare da tabbatar da cewa za su yi aiki tukuru cikin gaskiya da sadaukarwa domin cika alkawuran da suka ɗauka.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma yaba wa sakatarorin ƙananan hukumomi, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC), jami’an tsaro, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar gudanar da zaɓen.

A wani mataki na ƙarfafa harkokin gudanarwar ƙananan hukumomi da inganta ayyukan yi wa jama’a hidima, gwamnan ya miƙa sabbin motocin Toyota Hilux ga dukkan ƙananan hukumomi goma sha ɗaya da kuma sabbin Ƙananan Hukumomin Raya Karkara (LCDAs) da aka kafa a jihar.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci
Next Post: Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Fasalin Shirin NYSC

Karin Labarai Masu Alaka

TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika
APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika
Rundunar Sojin KTK Ta Harba Makami Teku Afrika
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya Amurka
Hukumar CAC Zata Dakatar da POS Mara Rijista a Kasar Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kamfanin NNPC Yana Tattaunawa Da Wani Kamfanin Kasar China Labarai
  • Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
  • Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai
  • Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
  • Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar Afrika
  • Takaddama Ta Barke Tsakanin Lebanon Da Isra’ila Akan Bakin Iyaka Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.