Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Takaddama Ta Barke Tsakanin Lebanon Da Isra’ila Akan Bakin Iyaka
Published: November 16, 2025 at 12:52 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Lebanon ta ce zata kai karar Isra’ila gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, a saboda wata katangar da ta gina ta kankare a bakin iyakar kudancin Lebanon, wadda ta tsallake bakin iyakar da majalisar ta shata dake raba tsakanin kasashen biyu.

Wannan iyakar da ake yi ma lakabi da Shudin Layi, MDD ce ta tsara shi domin raba tsakanin Lebanon da Isra’ila, da kuma Tuddan Golan na kasar Sham wadanda Isra’ila ta mamaye. Sojojin Isra’ila sun ja, suka koma bayan wannan layin a shekarar 2000 lokacin da suka janye daga kudancin Lebanon.

Wani kakakin babban sakataren MDD, Stephane Dujarric, yace wannan katanga ta Isra’ila ta sa wasu ‘yan kasar Lebanon ba su iya shiga wasu sassan yankunansu ba.

Ofishin shugaban Lebanon ya nanata wannan a lokacin da yake ci gaba da gina wannan katanga da Isra’ila keyi ya sabawa kuduri na 1701 na Kwamitin Sulhun MDD kuma ya keta haddin diyaucin kasar Lebanon,

A ranar Jumma’a, wani kakakin rundunar sojojin bani Isra’ila, ya musanta cewa wannan katanga da ake ginawa ta tsallake wannan layi da aka shata na iyaka.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza
Next Post: Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumomin Tsaron Najeriya Ne Suka Bukaci Amurka Ta Turo Musu Sojoji Amurka
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma’aikatan Jiha da Kwamishinoni 23 Afrika
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Amince Da Gyaran Fadar Sarkin Gombe Afrika
Shugaba Tinubu Ya Taya Murtala Garo Murnar Zama Mataimakin Gwamnan Kano Labarai
Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jaddada Haƙuri Da Fahimtar Juna A Siyasa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Yayi Magana Game Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Najeriya
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hankali Najeriya
  • Amurka Zata Fara Sayar Da Maganin Hana Kiba Da Jin Yunwa Amurka
  • An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo Wasanni
  • Somaliya: Ba Za Mu Dauki Wulakancin Donald Trump Ba! Sauran Duniya
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika
  • Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Senegal Yaki Amincewa Da Hukuncin CFA Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.