Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya
Published: November 17, 2025 at 3:11 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Ƙungiyar kwallon kafa ta Jamhuriyar Congo ta haramta wa Super Eagles ta Najeriya zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya (World Cup) 2026.

Jamhuriyar Congo ta samu nasara ne a wasan karshe da suka yi na neman cike gurbin zuwa gasar a bangaren afirka, inda ta doke Najeriya da ci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka kwashe minti casa’i da 1-1.

Wasan da aka yi shi a Rabar babban birnin Moroko. Yanzu dai Jamhuriyar Congo ita zata wakilci Africa a wasan da za’ayi na samun gurbi da sauran nahiyoyin inda za’a cire kasa daya da zata samu tikitin.

A nahiyar turai kuwa bangaren neman tikitin shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya. kasar Portugal ta lallasa Armenia da ci 9-1.

Dan wasan tsakiya na Arsenal, Gabriel Magalhaes, ya ji rauni a cinyarsa ta dama, yayin da yake buga wasa na ƙasa da ƙasa, saboda haka ba zai buga wasan sada zumunci da Brazil za ta buga da Tunisia a Faransa ranar Talata ba.

Dan wasan ya samu raunin ne a dai-dai minti 65 na wasan sada zumunci da Brazil tayi da Senegal a ranar Asabar a filin wasa na Emirates.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi. Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil (CBF) ta ce: “An sake duba ɗan wasan Arsenal, Gabriel Magalhaes, a ranar Lahadi (16) kuma an yi masa gwaje-gwajen hoto wanda ya nuna raunin tsoka a cinyarsa ta dama.

“Saboda haka, ɗan wasan ba zai yi tafiya tare da ƙungiyar zuwa wasan da za su yi a Lille ba. Gabriel, ya rufe fuskarsa da rigarsa cikin takaici yayin da yake barin filin wasa. Dan wasan baya mai shekaru 27 ya buga kowane minti a wasanni 11 na Premier League wa Arsenal a wannan kakar.

Gabriel ya taka muhimmiyar rawa a tarihin tsaron gidan Arsenal. Ita kuwa ƙungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake buga gasar La Liga a kasar Spain, tace bata yanke hukuncin sabunta kwantarakin dan wasan gaba na Poland Robert Lewandowski wanda kwantirakinsa  za ta ƙare nan bada jimawa ba.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/Labarin-Wasanni-GTA-Hausa.mp3
Wasanni

Post navigation

Previous Post: Takaddama Ta Barke Tsakanin Lebanon Da Isra’ila Akan Bakin Iyaka
Next Post: Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi

Karin Labarai Masu Alaka

Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025 Wasanni
An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Boko Haram Sun Farmaki Sansanin Sojoji A Borno Tsaro
  • Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
  • Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna Afrika
  • Majalisar Dokokin Filato Ta Kare Kudirin Alawus Ga Tsofaffin ‘Yan Majalisa Afrika
  • Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum Tsaro
  • Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
  • Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
  • Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.