Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ko Meye Gaskiyar Rade-Radin Zanga-Zanga A Jos Dake Jihar Filato
Published: March 6, 2026 at 1:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani sako cikin murya da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya tada hankalin mazauna garin Jos da kewaye.
Mai maganar, a cikin dakika talatin da takwas an jiyo shi yana shaida wa wani cewa kada ya fito daga gidanshi saboda za’a yi zanga-zanga a Jos.
Muryar da ta karade shafukan sada zumunta ta sanya fargaba a zukatan mutane da waswasin hana ‘ya’yansu zuwa makaranta da fita kasuwanci.
Kan haka ne kwamishinan ‘yan sanda na jihar Filato, Bassey Ewah ya kira taron gaggawa da matasan kungiyar Islamic Movement of Nigeria wato kungiyar Shi’a don jin karin bayani kan ko suna shirin yin tattaki ne, ganin yadda ya gudana a wassu jihohin Najeriya, biyo bayan yakin dake aukuwa tsakanin kasar Amurka da Isra’ila da Iran.
Adam Khalid Muhammad shine wakilin dalibai na kungiyar ‘yan’uwa Musulmi a Najeriya, reshen jihar Filato, dake karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-zakzaki yace sun shaida wa komishinan ‘yan sandan cewa basu san inda maganar zanga-zanga ta bullo ba.
Shima jagorar kungiyar a Jihar Filato, Sheikh Muhammad Auwal Abubakar yace kungiyarsu tana da tsari na mutunta ‘yancin kowa, don haka basu da niyyar tozarci ko kuntata wa kowa.
Rundunar ‘yan sandan ta jihar Filato dai ta kara tsaurara matakan tsaro a cikin garin Jos, musamman a unguwannin da take kira Flash Points, wato wuraren da ke da barazanar barkewar rikici, ciki har da kasuwanni.
Wakiyar Amurka Ke Magana a Jos Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton
https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/RADE-RADIN-ZANGA-ZANGA-A-JOS.mp3
Labarai

Post navigation

Previous Post: Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya
Next Post: Shugaban Najeriya Tinubu Ya Amince Na Tura Jakadu

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci Afrika
Masoya Kungiyar Kwallon Kafar Morocco Suna Cikin Farin Ciki Bisa Hukuncin Kotu Afrika
Shugaban Libya Ya Sayi Jirage Marasa Matuka Afrika
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
  • Amurka Ta Sanya Hanu Kan Yarjejeniyar Kiwon Lafiya Da Ƙasashen Madagascar, Saliyo, Botswana, Ethiopia Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Mauritius Zata Rage Amfani Da Makamashi Afrika
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Ya Roki Rasha Ta Taimakawa Kasar Afrika
  • Tinubu Ya Aika Manyan Hafsoshin Tsaro Borno Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.