Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tinubu Ya Aika Manyan Hafsoshin Tsaro Borno
Published: March 17, 2026 at 9:28 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa game da sabon harin ta’addanci da aka kai birnin Maiduguri na jihar Borno, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin bacin rai da ban takaici.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2026, Shugaba Tinubu ya jajantawa mutanen da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata, yana mai jaddada cewa gwamnati na tare da jama’ar Jihar Borno a wannan mawuyacin lokaci.

Shugaban ya bayyana cewa wadannan hare-hare na nuna alamun fargaba da matsin lamba da ’yan ta’addan ke fuskanta daga dakarun tsaron Najeriya.
“Wadannan ayyukan ta’addanci yunƙuri ne na ƙarshe na matsananciyar fargaba da waɗannan masu laifin ke yi domin dasa tsoro a zukatan mutane, sakamakon irin luguden wutar da suke fuskanta daga jami’anmu.” Inji Tinubu

Tinubu ya ƙara da cewa, a taron tsaro da ya gudanar a ƙarshen makon jiya, ya amince da samar da ƙarin kayan aiki da tallafin ayyuka ga hukumomin tsaro domin ƙarfafa dabarunsu na yaƙi da ta’addanci.

Domin tabbatar da an magance lamarin cikin gaggawa, Shugaba Tinubu ya ba wa manyan hafsoshin tsaro na ƙasa umarnin gaggawa na su koma birnin Maiduguri domin jagorantar ayyukan tsaro da kansu.

Haka kuma, ya umarci hukumomin agajin gaggawa da su tabbatar da sun ba wa duk waɗanda suka jikkata kulawar da ta dace.

A ƙarshe, Shugaban ya jaddada cewa babu wani lungu a Najeriya da zai zama wurin buya ga ’yan ta’adda, inda ya ce, “Ba za mu taba mika wuya ga tsoro ba. Za mu nemo su, mu fuskance su, kuma mu murƙushe su baki ɗaya.”

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Lauyoyi Sun Gurfanar Da Wani A Kotu Bisa Fasa Korin Kiyashi A Kenya
Next Post: Tinubu, Akpabio da Ministoci 9 Zasu Tafi Ƙasar Birtaniya

Karin Labarai Masu Alaka

NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
Ambaliyar Ruwa Yayi Ajalin Mutane A Nairobi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NLC Ta Yabawa Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Najeriya
  • An Kashe Sojojin Ukraine Dubu 55 A Kasar Rasha Afrika
  • Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti Afrika
  • Harin Iran A Kasar Saudiya Ya Haifar Da Tattaunawa Tsakanin Shugabanni Afrika
  • Matatar Man Dangote Zata Wadatar Da Najeriya Da Makota Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
  • Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar Amurka
  • Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Ya Roki Rasha Ta Taimakawa Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.