Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora
Published: April 6, 2026 at 7:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta sanar cewa za ta karɓi ‘yan ƙasashen waje da Amurka ke korar su daga ƙasar, ƙarƙashin wata sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Donald Trump, kamar yadda gwamnati a Kinshasa ta bayyana a cikin wata sanarwa jiya Lahadi.

Gwamnatin ta ce za ta fara karɓar waɗanda aka kora daga watan Afrilu, amma ba ta bayyana adadin mutanen da ta amince za ta karɓa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka ce za ta ɗauki nauyin wannan shiri gaba ɗaya, ba tare da wani kuɗi daga gwamnatin Kongo ba. Haka kuma, an tanadi wuraren zama kusa da babban birnin ƙasar, wato Kinshasa, domin sauƙaƙa wa waɗanda za a kawo masauki.

Amurka ta riga ta tura wasu ‘yan ƙasashen waje da aka kora zuwa wasu ƙasashen Afirka da suka haɗa da Ghana, Cameroon, Equatorial Guinea da Eswatini, lamarin da ya janyo suka daga masana harkokin doka da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.

Wannan yarjejeniya na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Kongo da Rwanda, tare da wata yarjejeniya da ke tabbatar da samun damar Amurka ga muhimman ma’adanan Kongo.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu
Next Post: Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya Afrika
Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
NEDC Ta Karyata Bada Tallafin Karatun MSc Da Ke Yawo A Kafafen Sadarwa Afrika
INEC: Akwai Yiwuwar Dage Zaben 2027 Saboda Azumi Labarai
RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
  • Rikicin Aure: Albani Agege Ya Zargi Sheikh Gumi Da Boye Matarsa ‘Yar Morocco Afrika
  • Hukumar ICPC Ta Kwato Makudan Kudade Rediyo
  • Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Karbi Shaidar Jam’iyar APC Siyasa
  • Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
  • Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Messi Da Cristiano Suna Da Tasiri A Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.