Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Majalisar Dokokin Filato Ta Kare Kudirin Alawus Ga Tsofaffin ‘Yan Majalisa
Published: July 21, 2026 at 12:37 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Dokokin jihar Filato ta yi karin haske kan kudirin dokar da ke neman samar da tsarin alawus na wata-wata ga tsofaffin ‘yan majalisar jihar, bayan ce-ce-ku-cen da kudirin ya haifar a tsakanin al’umma.

A makon da ya gabata ne majalisar ta gabatar da kudirin dokar, wanda ya tsallake karatu na farko da na biyu a rana guda. Kudirin na neman bai wa tsofaffin shugabannin majalisa da mambobin da suka kammala wa’adinsu damar samun alawus na wata-wata mai kama da pansho.

Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dokokin Jihar Filato, kuma mamba mai wakiltar Rukuba/Irigwe, Eli Bako Ankala, wanda ya gabatar da kudirin, ya ce manufarsa ita ce ‘yan majalisar da ke kan mulki su ware wani kaso daga alawus dinsu domin tallafa wa tsofaffin ‘yan majalisar.

Ya bayyana cewa kudaden ba za su fito daga gwamnatin zartarwa ba, sai dai daga gudunmawar da ‘yan majalisar za su rika bayarwa daga alawus dinsu.

Sai dai kungiyoyin farar hula da na kwadago a jihar sun yi watsi da kudirin, suna zargin cewa ba a bayyana cikakkun bayanansa ga jama’a ba.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Filato, Kwamared Eugene Manji, ya ce sun bai wa majalisar wa’adin zuwa ranar 30 ga watan Yuli ta janye kudirin, yana mai gargadin cewa idan ba a yi hakan ba, za su dauki matakin kulle harabar majalisar.

A halin yanzu dai ana ci gaba da sa ido kan yadda rikicin ra’ayi tsakanin majalisar da kungiyoyin farar hula da na kwadago zai kaya idan wa’adin ya cika.

Daga Jos, Zainab Babaji ta aiko mana da rahoto

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/07/AUD-20260721-WA0024.mp3
Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Jaddada Buƙatar Kare Rayukan ‘Yan Afirka A Taron ECOWAS
Next Post: Kungiyar Miyetti Allah Ta Bukaci Mambobinta Su Marawa Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna Baya A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Wajen Hakar Ma’adanai Dake Jihar Filato Najeriya
Mutane Da Yawa Ke Mutuwa A Dalilin Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba Kiwon Lafiya
Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin Afrika
Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama Afrika
  • Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila Afrika
  • Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan Labarai
  • Togo Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Burkina Faso Saboda Kitsa Juyin Mulki Afrika
  • Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC Siyasa
  • Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
  • Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.