Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan
Published: April 2, 2026 at 2:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 2, 2026

Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin Kaduna Electricity Distribution Company domin inganta samar da wutar lantarki a faɗin jihar.

Sakataren Gwamnatin jihar, Yakubu Bala Tafida ne ya bayyana hakan yayin da yake cikin tawagar gwamnatin jihar da ke halartar wani muhimmin taron makamashi da ke gudana a birnin London na ƙasar Birtaniya.

A cewarsa, yarjejeniyar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin an samu ingantacciyar wutar lantarki ga al’ummar Kebbi, wanda ake sa ran zai ƙarfafa harkokin tattalin arziki, jawo zuba jari, tare da inganta rayuwar jama’a.

Gwamnan ya halarci taron tare da wasu takwarorinsa da suka haɗa da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, inda suka tattauna kan hanyoyin bunƙasa zuba jari a fannin makamashi da ci gaban yankuna.

Taron ya haɗa manyan jami’an gwamnati, ƙwararru a fannin makamashi da masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin inganta rarraba wutar lantarki a yankin da KEDCO ke aiki.

Gwamnatin Kebbi ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki na inganta ababen more rayuwa da samar da yanayi mai kyau ga ci gaba, daidai da tanade-tanaden dokar lantarki ta shekarar 2023 da ke ƙarfafa shigar kamfanoni masu zaman kansu a fannin.

Gwamnatin ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye shiryen da za su amfani al’umma, inda wannan haɗin gwiwa a fannin lantarki ke daga cikin muhimman matakan da take ɗauka.

Afrika, Labarai, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos
Next Post: Shugaba Trump Yace Babu Maganar Kawo Karshen Yakin Amurka Da Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja Labarai
Kasar Jamus Ta Haramtawa Yara Kasa Da Shekaru 14 Hawa Dandalin Sada Zumunta Labarai
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Shugabannin Kasashen Afirka Ta Tsakiya Sun Kamallah Taron Koli Afrika
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yanbindiga sun Kashe mutun guda tare da yin garkuwa da mutane kimanin 100 a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • Jam’iyar APC A Jihar Gombe Ta Tsayar Da Jamilu Isiyaku Gwamna Takarar Gwamna Afrika
  • Akwai Shakku Akan Sanin Wacce Kungiyar Kwallon Kaface Zata Lashe Gasar Kofin Afirka Da Akeyi A Morocco Nishadi
  • Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Hikima Da Jagorancin Sarkin Gombe A Shekaru 12 Na Jagoranci Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.