Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Kungiyar Miyetti Allah Ta Bukaci Mambobinta Su Marawa Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna Baya A Gombe
Published: July 22, 2026 at 2:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore a jihar Gombe ta bayyana goyon bayanta ga Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna, wanda aka fi sani da Sardaunan Gombe, a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027

Shugaban ƙungiyar a jihar, Ardo Chindo Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da makiyaya da manoma a Masarautar Bojude da ke Ƙaramar Hukumar Kwami.

Taron ya gudana ne a lokacin da tawagar yaƙin neman goyon bayan Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna ƙarƙashin jagorancin Dakta Ahmad Muhammad Gana ta kai ziyara yankin

Ardo Chindo ya ce manufar ziyarar ita ce ƙarfafa zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma tare da samar da mafita ga rikice-rikicen da suka daɗe suna faruwa tsakanin al’ummomin Fulani a yankin. Ya kuma buƙaci mazauna yankin su ci gaba da zama lafiya domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Da yake jawabi, jagoran tawagar yaƙin neman goyon baya, Dakta Ahmad Gana, ya bayyana Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin mutum mai tawali’u, tausayi da ƙwarewa wajen gudanar da aiki. Ya ce ya taimaka wa mutane da dama a lokacin da yake aiki a Hukumar Samar da Ruwa ta Jihar Gombe da kuma Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO).

Ya yi kira ga al’ummar jihar Gombe da su marawa Dakta Gwamna baya, yana mai cewa jajircewarsa, gaskiyarsa da sadaukarwarsa wajen taimakon talakawa sun cancanci a ba shi damar jagorantar jihar.

Shi ma Shugaban Hukumar Ci Gaban Ƙaramar Hukumar Kwami ta Yamma (Kwami West LCDA), Sa’ad Abdulmumini, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar APC da ‘yan takararta, yana mai cewa ayyukan ci gaban da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aiwatar sun ƙara wa jam’iyyar karɓuwa a wajen al’umma.

A nasa jawabin, Hakimin Bojude, Alhaji Muhammad Ibrahim Dan Buram, ya lissafo wasu ayyukan raya ƙasa da aka aiwatar a masarautarsa, ciki har da gina fadar hakimi, hanyoyi, fitilun tituna masu amfani da hasken rana da kuma kafa hedikwatar Hukumar Ci Gaban Ƙaramar Hukumar Kwami ta Yamma a Bojude.

Hakimin ya sake jaddada goyon bayansa ga Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna da sauran ‘yan takarar APC, yana mai bayyana fatan cewa za su ci gaba da kawo ribar dimokuraɗiyya ga al’ummar Jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Majalisar Dokokin Filato Ta Kare Kudirin Alawus Ga Tsofaffin ‘Yan Majalisa
Next Post: An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan Labarai
Shugaban Najeriya Tinubu Ya Amince Na Tura Jakadu Labarai
Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku Labarai
Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
  • Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
  • Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Amince Da Tsagaita Wuta Labarai
  • Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
  • Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.