Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026
Published: July 13, 2026 at 10:42 PM | By: Bala Hassan

An Fara Gasar Bauchi Annual International Polo

A ranar litinin 13 ga watan Yulin 2026 ne aka ƙaddamar da gasar Bauchi Annual International Polo Tournament 2026 a filin wasan Col. AD Umar Polo Ground da ke kan titin Ningi a jihar Bauchi a tarayyan Najeriya.

Bikin buɗe gasar ya samu halartar manyan baƙi, masu ruwa da tsaki a harkar wasan polo, shugabannin ƙungiyoyi da dimbin sha’awar wasan daga sassa daban-daban na Najeriya, da kuma kasashen waje lamarin da ya nuna muhimmancin gasar a matsayin na ɗaya daga cikin manyan wasannin polo da ake gudanarwa a ƙasar.

A wannan shekara, ana sanya manyan kofuna guda huɗu da suka haɗa da Governor’s Cup, Emir of Bauchi Cup, Tafawa Balewa Cup da kuma Sarkin Fulani Cup, ƙungiyoyi da ‘yan wasa daga jihohi daban-daban ne za su nuna bajinta a tsawon kwanakin da za’a yi a gasar inda aka fara tun ranar 13 har zuwa 18 ga Yuli, 2026.

Jami’in hulda da jama’a na gasar Shamsuddeen Marafa, ya bayyana wa GTA Hausa cewa, baya ga nishaɗi wasan na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin yawon buɗe ido, kasuwanci da kuma hada zumunci tsakanin mahalarta daga sassa daban-daban na ƙasar har da na ketare.

A bana an samu karin ƙungiyoyi masu buga gasar Polo fiye da na shekarun baya wadda hakan ya ke nuna irin nasarorin da ake cimmawa wajan hada wannan gasar tare da taimakon yan Kasuwa da kuma Gwamnati da dai-dai kun al’uma ” Shamsudeen.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: CP Chuso Ya Yaba da Matakan Gwamnatin Gombe Wajen Rage Rikicin Makiyaya Da Manoma
Next Post: Jami’an Tsaro Sun Dakile Safarar Makamai Daga Jos Zuwa Jihar Neja

Karin Labarai Masu Alaka

Lawal, Filin Wasa Na Rashidi Yekini Ko Turai Iyaka Wasanni
Nasarawa Ce Zakara A Wasan Kwallon Kafa Ta Kurame 2025 Wasanni
AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kamaru Ta Lallasa Malawi 3-0, Ta Lashe Kofin WAFCON Na Farko A Tarihi Wasanni
Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
  • Kotun Tarayya Tabada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni
  • Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
  • Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.