Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini Afrika
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji Afrika
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika

INEC Ta Ce Ta Kammala Shirye-Shiryen Zaɓen Cike Gurbi A Gombe
Published: September 15, 2026 at 1:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: September 15, 2026

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta a Najeriya wato INEC, ta ce ta kammala shirye-shiryenta domin gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Gombe, Kwami da Funakaye, wanda za a gudanar ranar Asabar.

Kwamishinan Zaɓe na jihar Gombe, Alhaji Umar Mukhtar Gajiram, ne ya bayyana hakan yayin taron Kwamitin Tuntuɓa kan Tsaron Zaɓe na Ƙungiyoyin Hukumomin Tsaro, ICCES, da aka gudanar domin duba shirye-shiryen zaɓen.

Alhaji Gajiram ya ce hukumar ta karɓi dukkan kayan zaɓe marasa muhimmanci da ake buƙata, yayin da aka kammala horas da jami’an kula da masu jagorantar rumfunan zaɓe, wato Supervisory Presiding Officers.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da horas da Presiding Officers da Assistant Presiding Officers, yayin da hukumar ke jiran isowar kayan zaɓe masu muhimmanci.

Kwamishinan ya jaddada buƙatar samar da isasshen tsaro domin kare jami’an INEC da kayan zaɓe a rumfunan zaɓe 903 da ke faɗin ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye.

Ya bayyana Gombe da Funakaye a matsayin wuraren da ake ɗauka a matsayin masu haɗarin tsaro, sakamakon ayyukan ’yan daba masu alaƙa da siyasa.

Saboda haka, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen tattara bayanan sirri, gano alamun barazana tun da wuri da kuma gaggauta ɗaukar matakin da ya dace idan wata barazana ta taso.

Shi ma da yake magana, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, kuma mataimakin shugaban kwamitin ICCES, CP Umar Ahmed Chuso, ya ce an ɗauki matakan tsaro na riga-kafi domin magance matsalolin tsaro da aka gano kafin da kuma lokacin zaɓen.

CP Chuso ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su gudanar da harkokinsu cikin lumana, yana mai gargadin cewa jami’an tsaro ba za su lamunci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali ba.

Taron INEC da ICCES ya haɗa wakilan hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbin cikin lumana, gaskiya da sahihanci ranar Asabar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Gombe Ta Raba Naira Miliyan 14 Ga Iyalen ‘Yan Jaridan Da Suka Rasu Najeriya
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • INEC Ta Ce Ta Kammala Shirye-Shiryen Zaɓen Cike Gurbi A Gombe
  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas Afrika
  • Dan Wasan Gaba Na Manchester United, Zirkzee Ya Amince Da Komawa Juventus Ko Napoli Wasanni
  • Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan Labarai
  • Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa Labarai
  • Kasar Amurka Ta Sayi Kamfanin Sada Zumunci Na Tik-Tok Amurka
  • Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba Amurka
  • Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.