Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa
Published: May 29, 2026 at 9:42 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: May 29, 2026

Mai Martaba Sarkin Gombe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Gombe, Alhaji (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III, ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa abin da ya bayyana a matsayin shekaru bakwai na shugabanci mai cike da sauyi da ci gaba a fadin jihar Gombe.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin gaisuwar Sallah da Majalisar Masarautar Gombe ta kai wa gwamnan a gidan gwamnatin jihar da ke Gombe.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Mai Martaban ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya cika alkawarin da ya dauka na aiki domin ci gaba da wadata a jihar, yana mai cewa nasarorin gwamnatin sun bayyana karara a muhimman fannoni da suka hada da gine-ginen more rayuwa, ilimi, lafiya, tsaro, bunkasa tattalin arziki, kare muhalli da kuma sabunta birane.

Ya bayyana shekaru bakwai na gwamnatin Inuwa Yahaya a matsayin lokaci na gagarumin sauyi da ci gaba mai dorewa a dukkan sassan jihar.

Sarkin ya yabawa gwamnatin kan kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, yana mai cewa kafa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ya taimaka wajen karfafa tsarin tsaro tare da tabbatar da Gombe a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.

Haka kuma, Sarkin ya bayyana wasu daga cikin manyan ayyukan raya kasa da gwamnatin ta aiwatar da suka hada da yankin Three-Arms Zone, Muhammadu Buhari Industrial Park, Agro-Livestock Development Zone, katafaren mayanka na zamani, tashar Inland Dry Port, ayyukan magance zaizayar kasa, hanyoyi, fadada samar da ruwa, manyan makarantu da cibiyoyin lafiya.

Ya kuma yabawa gwamnatin kan shirye-shiryen sabunta birane da suka hada da gina Shehu Abubakar District da kuma gina gadar karkashin kasa ta farko a jihar, tare da ayyukan tsaftar muhalli da kawata birane.

Mai Martaban ya sake tabbatar da goyon bayan masarautar ga gwamnatin jihar tare da kira ga al’umma da su ci gaba da mara wa gwamnati baya domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaba.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma a Jihar Gombe.

Gwamnan ya gode wa Sarkin da Majalisar Masarautar Gombe bisa ziyarar da kuma goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa, yana mai bayyana sarakunan gargajiya a matsayin muhimman abokan hulda wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a matakin al’umma.

Ya ce gwamnatinsa ta samu manyan nasarori cikin shekaru bakwai da suka gabata a fannoni daban-daban, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da amfani da albarkatun jihar yadda ya kamata domin inganta rayuwar jama’a.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma jaddada cewa ci gaba aiki ne mai dorewa da ke bukatar hadin kai, fahimtar juna da goyon bayan jama’a baki daya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi
Next Post: Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
Kwankwaso: Gwamnatin Kano Tamuce Baki Daya, Tafiya APC Allah Ya Raka Taki Gona! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi Labarai
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya Afrika
  • Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Da Suka Kifar Da Farar Hula A Guinea-Bissau Sun Sanar Da Cewa! Afrika
  • Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.