Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Gombe: Babu Hannun mu a Cin Zarafin Kansilan Mazabar Shamaki
Published: December 20, 2025 at 9:45 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Gombe ta musanta zargin da ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi cewa, ana cin zarafi ko wulaƙanta waɗanda suka soki gwamnatin jahar.

Wata sanarwar da kakakin gwamnatin jahar Ismaila Uba Misilli ya fitar da yammacin Juma’a, ta ce babu ƙamshin gaskiya a zargin da ƙungiyar ta yi bayan wani faifan bidiyo ya nuna ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar yana marin Kansilar gundumar Shamaki.

A sanarwar, Misilli ya ce bai kamata a riƙa alaƙanta lamarin da gwamnatin jihar ba, har ma ya yi gargaɗi game da saka siyasa kuma ya nesanta hannun wani jami’in gwamnati ko gwamnatin jhar a ciki.

Sanarwar ta ce babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma tuni aka fara ɗaukar matakan bincike dan ɗaukar mataki kan lamarin da ya sha suka daga al’umma.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa a guji alaƙanta lamarin da gwamna ko gwamnatin jihar, tana mai cewa Gwamna Inuwa Yahaya baya goyon saɓa doka ko cin mutuncin wani.

A yanzu dai ƙungiyoyin da al’umma na jiran ganin matakin da gwamnatin za ta ɗauka a kan wanda ake zargin.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda
Next Post: Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi

Karin Labarai Masu Alaka

Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
Magoya Bayan Tijjaniyya Zasu Kauracewa Zabe Saboda Kama Sheikh Sani Khalifa Afrika
Ranar Lahadi Anyi Zaben Shugaban Kasa A Congo Afrika
Ministan Sufurin Najeriya Ya Ajiye Mukaminsa Domin Takarar Gwamna Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika
  • Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB Siyasa
  • Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
  • FIFA Ta Ba Da Goyon Bayanta Ga Gyaran Ƙwallon Ƙafa A Najeriya, Shehu Dikko Ya Gana Da Infantino Wasanni
  • An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026 Afrika
  • FIFA Ta Buɗe Bincike Kan Koci Hossam Hassan Na Masar Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.