Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno
Published: July 12, 2026 at 2:09 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rabawa mambobin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke aiki a ƙananan hukumomin Bayo da Hawul tallafin kuɗi da ya kai jimillar naira miliyan 8 da dubu 200 (N8.2m), a wani mataki na ƙarfafa musu gwiwa.

A ƙaramar hukumar Bayo, Gwamna Zulum ya bai wa kowane ɗaya daga cikin mambobin NYSC 29 kuɗi naira dubu hamsin (N50,000). Haka kuma, ya bai wa Corps Liaison Officer (CLO) da Local Government Inspector (LGI) naira dubu ɗari (N100,000) kowannensu. Jimillar kuɗin da aka rabawa a ƙaramar hukumar ta Bayo ta kai naira miliyan 1 da dubu 650 (N1.65m).

A ƙaramar hukumar Hawul kuwa, Gwamnan ya bai wa kowane ɗaya daga cikin mambobin NYSC 125 naira dubu hamsin (N50,000), yayin da Corps Liaison Officer (CLO) ya karɓi naira dubu ɗari (N100,000), sannan Local Government Inspector (LGI) ya karɓi naira dubu ɗari biyu (N200,000). Jimillar kuɗin da aka raba a Hawul ta kai naira miliyan 6 da dubu 550 (N6.55m).

Gaba ɗaya, ƙananan hukumomin Bayo da Hawul sun amfana da tallafin da ya kai naira miliyan 8 da dubu 200 (N8.2m).
Da yake tsokaci kan wannan tallafi, Kodinetan Hukumar NYSC na jihar Borno, Malam Nasir Bello, ya bayyana jin daɗinsa, yana mai cewa wannan karamci bai zo masa da mamaki ba, domin ya zama al’adar Gwamna Zulum na kula da jin daɗin mambobin NYSC.

Ya ƙara da cewa, ci gaba da ba da muhimmanci ga walwala da jin daɗin mambobin NYSC a jihar Borno zai ƙara jawo hankalin matasa masu yi wa ƙasa hidima su karɓi aiki a jihar cikin kwarin gwiwa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: PDP Ta Nemi Bincike Kan Rushewar Ginin Majalisar Dokokin Gombe, Tayi Zargi Game Da Sakaci
Next Post: An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo

Karin Labarai Masu Alaka

Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan Labarai
Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya Labarai
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
  • Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
  • Najeriya Zata Kara Mai Da Take Hakowa Afrika
  • Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
  • Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland Amurka
  • Gaza Ga Albarusai Ga Yunwa Tsaro
  • Akwai Bukatar Bin Dokokin Tuki A Kan Hanyoyi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.