Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe
Published: April 2, 2026 at 9:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 3, 2026

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe na sanar da daukacin jama’a cewa, bayan wani muhimmin taron tsaro da aka gudanar tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki, an yi cikakken nazari kan halin tsaro da ake ciki a jihar.

Sanarwar Jami’in hulda da jama’a na Rundunar DSP Buhari Abdullahi ta bayyana cewa, Bayan tattaunawa mai zurfi da kuma nazari kan matsalolin tsaro da ke akwai, an cimma matsaya cewa za a ci gaba da aiwatar da takaita amfani da babura a cikin birnin Gombe. Wannan takaita zai ci gaba da aiki daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a kowace rana, kuma za a fara sake aiwatar da shi daga ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, 2026.

An dauki wannan mataki ne domin hana amfani da babura wajen aikata laifuka da kuma kara inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Rundunar na godiya da hadin kai da fahimtar da jama’a masu bin doka suke nunawa, tare da kira ga kowa da kowa da ya bi wannan umarni domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Haka kuma, ana karfafa gwiwar jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi ko aiki mai tayar da shakku ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Za a ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba dangane da wannan batu.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Birai
Next Post: Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
Prime Ministan Pakistan Yace Zai Karbi Bakoncin Tattaunawar Amurka Da Iran Afrika
Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Gabatar Da Gwajin Makami Mai Linzami Afrika
Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
Mabiya Addinin Kirista Da ‘Yan Bindiga Suka Sace Sun Kubuta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Kasar Faransa Ya Zanta Da Shugaban Kasar Iran Afrika
  • Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika
  • Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa Labarai
  • Makarantun Allo Zasu Yi Gogayya Da Na Boko Labarai
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
  • Turkiyya Ta Zargi Alakar Isra’ila Da Somaliya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.