Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ƙarin Albashi Zai Fara Aiki Ga Sojojin Najeriya Daga Satumba
Published: August 5, 2026 at 8:14 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙarin albashi ga jami’an Rundunar Sojin Najeriya da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce na inganta jin daɗin jami’an tsaro da ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ta bayyana cewa kimanin jami’ai da sojoji 250,000 ne za su amfana da sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumban 2026.

A cewar sanarwar, jami’an da ke daga mukamin Birgediya Janar zuwa Janar za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin ɗari. Waɗanda ke daga mukamin Kanal zuwa Warrant Officer kuma za su samu ƙarin kashi 50 cikin ɗari, yayin da sojojin da ke daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant za su amfana da ƙarin albashi mafi girma na kashi 80 cikin ɗari.

Sabon tsarin albashin zai ƙara yawan kuɗin da gwamnatin tarayya ke kashewa kan albashin jami’an rundunar sojin daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924 a shekara.

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na yaba wa jajircewa da sadaukarwar jami’an rundunar sojin wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan ƙasar.

Ya ce jami’an tsaro sun cancanci tallafi da yabo saboda rawar da suke takawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗinsu tare da samar musu da makamai da fasahohin zamani domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Shugaban ƙasar ya kuma jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba mai ɗorewa ba tare da ingantaccen tsaro ba, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da dukkan rundunonin tsaro wajen yaƙi da barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya buƙaci jami’an rundunar sojin da su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin alamar godiya daga gwamnati, tare da bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa Najeriya za ta yi nasara kan masu neman tada zaune tsaye da tarwatsa zaman lafiyar ƙasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe
Next Post: NANPAN Ta Wayar Da Al’umma Kan Amfanin Shayar Da Jarirai Nono Kaɗai

Karin Labarai Masu Alaka

Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central Afrika
Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko Najeriya
Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
Hukumomin Taliban Sunce A Shirye Suke Domin Sulhu Afrika
An Fara Azumin Watan Ramadan A Najeriya Da Sassan Duniya  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Birnin Niamey Labarai
  • Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Matsalar Tsaro A Shiyar Labarai
  • An Fara Dawo Da Alhazain Najeriya Gida Afrika
  • Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai
  • Ministan Kudin Botswana Yace Akwai Hasashen Cewa Tattalin Arzikin Kasar Zai Ragu Amurka
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
  • Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.