Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwar Zamani a Najeriya (NITDA) ta zaɓi Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci Gaba (CITAD) domin ba ta lambar yabo ta musamman bisa gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ilimin amfani da fasahar dijital, inda ta horas da mutane 22,563, ciki har da mutane 610 masu nakasa.
Ana sa ran miƙa lambar yabon ne a yayin taron ƙasa na DL4ALL na shekarar 2026, wanda za a gudanar a ranar Talata, 20 ga Oktoba, a Cibiyar Albarkatun Dijital ta Hukumar Ilimi Bai Ɗaya (UBEC), da ke unguwar Kado a Abuja.
A cikin saƙon imel da ya aika wa CITAD domin sanar da ita zaɓen, Mataimakin Darakta a Sashen Bunƙasa Ayyukan Dijital na NITDA, Injiniya Ahmed Yusuf Tambuwal, ya ce lambar yabon na nuna amincewar hukumar da ƙoƙarin ƙungiyar wajen tabbatar da cewa kowa ya samu damar koyon amfani da fasahar dijital.
NITDA ta buƙaci ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke inganta ilimin dijital da su yi rajista a manhajar tare da gabatar da bayanan ayyukan horaswar da suke gudanarwa da tasirinsu ga al’umma.
Shirin DL4ALL na tattara sahihan bayanan horaswa daga hukumomin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin farar hula da abokan hulɗa na ci gaba domin samar da kundin bayanai guda ɗaya da zai nuna mutanen da ake horaswa, wuraren da ake gudanar da horaswar, da hanyoyi da ƙa’idojin da ake amfani da su a jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar.
Ana sa ran wannan manhaja za ta taimaka wajen inganta haɗin kai, sa ido da kuma tantance tasirin shirye-shiryen koyar da ilimin dijital a faɗin Najeriya.
CITAD ƙungiya ce mai zaman kanta da ke da hedikwata a Kano, wadda ke inganta amfani da fasahar sadarwa da bayanai wajen samun ci gaba mai ɗorewa, haɗa kowa cikin amfani da fasahar dijital da inganta shugabanci na gari, musamman a al’ummomin da ba sa samun isasshen kulawa da damammaki.


