Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba
Published: March 16, 2026 at 8:57 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasar Afirka ta Kudu tace bata da wani dalili da zata yanke alaka da Iran, a cewar darakta janar na harkokin wajen kasar, bayan da aka ce sabon jakadan Amurka na kasar yace alakar Afirka ta Kudu da Iran zai iya kawo cikas wajen kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar da Amurka

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, a karshen mako, darakta janar na harkokin wajen Afirka ta Kudu, Zane Dangor, ya kuma yi watsi da wasu bukatun gwamnatin Donald Trump, kamar Janye tuhumar kisan kare dangi da kasar ke yiwa Isra’ila, soke shirin karfafa al’ummar bakar fata, da kuma karban shirin tallafin ‘yan gudun hijira na fararen fata.

A watan Augustan shekara data gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa Afirka ta kudu kashi 30 cikin 100 na harajin kayan fito daga kasar, abinda zai iya jawo mutane su rasa ayyukan su, kuma a lokacin da kashi uku na mutanen kasar basu da aikin yi. Sannan kuma alakar kasar da Amurka tayi tsami tun bayan da Trump ya zargi gwamnatin kasar da cin zarafin fararen fata, da ikirarin ana kwacewa manoman su filaye.

Afrika, Amurka, Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha
Next Post: Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya Na Shafar Harkokin Jinya A Asibitoci Kiwon Lafiya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jami’ar ABU Zaria Ta Karbi Kudade Naira Bilyan 1.3 Daga Shirin Nelfund Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
  • Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP Siyasa
  • CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
  • Jam’iyyar ADC Ta Karbi Peter Obi Da Wasu Manyan ‘Yan-Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Botswana Na Samun Kudaden Shiga Da Lu’ulu’u Labarai
  • Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
  • ‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.