Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu
Published: April 22, 2026 at 5:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Filato ta gurfanar da mutane biyar a gaban kotu da take zargi da kai hari da kisan mutane fiye da talatin a Anguwar Rukuba dake karamar hukumar Jos ta Arewa.

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne gwamnatin jihar Filato ta shigar da karar wassu mutane biyar a gaban kotu, wanda jami’an tsaro na farin kaya ta DSS suka kama, bisa zargin kashe mutane fiye da talatin a karshen watan Maris na wannan shekara, a Anguwar Rukuba dake karamar hukumar Jos ta Arewa.

Gwamnatin ta shigar da karar mutane hudu daga cikinsu kan laifin ta’addanci, yayinda mutum guda ake tuhumarsa da laifin hadin baki, kisa, mallakar makamai da safarar makamai da albarusai ba bisa ka’ida ba.

Da yake gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, babban lauyan jihar, Philemon Audu Daffi yace laifin da mutanen suka aikata ya saba wa sashe na 269 da sashe na 270 na dokar Penal code na jihar Filato.

Rahoton da kakakin rundunar dake aikin wazadda zaman lafiya a jihar Filato ta Operation Enduring Peace, Chinonso Oteh ya aike wa manema labarai, bai bayyana ranar da za’a ci gaba da sauraron karar ba.

A halin da ake ciki dai, yayinda zaman lafiya ya dawo cikin birnin Jos, wassu da suka tsira da lafiyarsu, a lokacin tashin hankalin, sun bayyana cewa mabiya addinan da ba nasu ba sune suka boye su, don kar a hallaka su.

Malama Martha Kura tace ta gamu da fusatattun matasa ne yayinda ta fito kasuwa, amma al’ummar musulmi dake wurin suka kareta.

Shima Alhaji Nasiru Muhammad Ali wanda rikicin ya rutsa da shi a unguwar Eto-Baba, dake kusa da Anguwar Rukuba yace kirista ne suka boye shi.

Al’ummar jihar Filato dake son zaman lafiya dai suna kan fadakar da jama’a muhimmancin kyakkyawar hulda da zamantakewa don samun ci gaba.

Ga Rahoton Zainab Babaji Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/AUD-20260422-WA0056.mp3
Afrika, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci
Next Post: Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
Gwamnatin Jihar Kano Zata Kashe Makudan Kudade Ga Jama’ar Kano! Najeriya
Anyi Asarar Biliyoyin Naira A Gobarar Kasuwar Singa Labarai
Jam’iyar SDP Tana Gudanar Da Babban Taro A Bauchi Afrika
Shugaban Kasar Faransa Ya Zanta Da Shugaban Kasar Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wani Abu Ya Fashe A Asibitin Bagudo Dake Jihar Kebbi Tsaro
  • Nnamdi Kanu Zai Daukaka Kara Har Zuwa Kotun Koli Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20 Afrika
  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika
  • Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
  • Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark Afrika
  • Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.