Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Rikicin Aure: Albani Agege Ya Zargi Sheikh Gumi Da Boye Matarsa ‘Yar Morocco
Published: September 5, 2026 at 6:34 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: September 5, 2026

Wani mazaunin jihar Kaduna kuma Shugaban tawagar Qausain Alhaji Nasiru Musa Idris (Albani Agege) ya zargi fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, da raba shi da matarsa ‘yar kasar Morocco, wadda ya ce ta kwashe kusan watanni 11 ba tare da ya samu damar tuntubarta ba.

Nasir Albani Agege ya bayyana hakan ne a wata hira da RFI Hausa, inda ya ce ya kai matarsa wajen Sheikh Gumi ne domin ba ta shawarar addini, bayan malamin ya bukaci ya kawo masa ita.

Ya ce kafin wannan lokaci, ya amince da Sheikh Gumi a matsayinsa na malamin addini, shi ya sa bai ga wani laifi ba wajen kai matarsa gare shi domin neman shawara.

A cewarsa, bayan matar tasa ta gana da Sheikh Gumi, ta daina amsa kiransa, lamarin da ya ce ya sa ya fara kokarin gano inda take tare da neman taimakon hukumomin tsaro.

Idris Albani Agege ya kuma yi zargin cewa kokarin da hukumomin tsaro suka yi na binciken lamarin ya fuskanci cikas.

Ya ce matarsa ba ta taba sanin Sheikh Gumi ba kafin ya gabatar da ita gare shi, yana mai cewa shi ne kadai ya san malamin kuma ya kai ta wajen Gumi ne saboda ya amince da shi.

Haka kuma, Idris ya ce matsalar ta fara ne bayan Sheikh Gumi ya bukaci ya sake samun wata takardar aure daga kotun Shari’a, duk da cewa yana da takardun aure da aka bayar a Morocco da Najeriya.

Ya ce ya gabatar da takardun da suka shafi aurensu, ciki har da wasu takardu daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da ofishin jakadancin Najeriya a Morocco, da kuma rahoton binciken halayyar mutum daga ‘yan sanda.

Idris ya kara da cewa daga bisani ya yi zargin cewa Sheikh Gumi ya fara kokarin ganin an raba auren, tare da cewa ya nemi malamin da ya amsa gayyatar ‘yan sanda domin a gudanar da bincike kan lamarin.

Sai dai Sheikh Ahmad Gumi ya musanta zargin.

Da yake magana da Daily Trust, Sheikh Gumi ya ce matar ta riga ta bar Najeriya, kuma tana kasar Morocco tare da iyayenta cikin kwanciyar hankali.

Malamin ya kuma ce ba ya son yin karin bayani kan lamarin saboda batun yana gaban kotu, amma ya yi barazanar kai Albani Agege kotu bisa zargin bata masa suna.

Shi ma Nasiru Ayuba, wanda aka fi sani da Dan Agaji, kuma mataimaki na musamman na Sheikh Gumi, ya musanta zargin cewa malamin ya tsare matar a gidansa.

Ayuba ya ce matar ce da kanta ta je wajen Sheikh Gumi domin neman taimako kan wata matsala ta kashin kanta, inda malamin ya yi kokarin taimaka mata tare da kai lamarin gaban kotu.

Ya kuma zargi Idris da kokarin bata sunan Sheikh Gumi ta kafafen sada zumunta.

A halin yanzu, lamarin ya zama rikici tsakanin bangarorin biyu, yayin da Idris ke neman a gudanar da bincike kan inda matarsa take da kuma yadda aka raba su, shi kuma Sheikh Gumi ya musanta zargin tare da cewa zai dauki matakin shari’a kan zargin bata masa suna.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Diphtheria: Mutane 23 Sun Mutu A Jihar Filato
Next Post: Gombe Ta Zo Ta Biyu Wajen Aiwatar Da Shirin L-PRES

Karin Labarai Masu Alaka

Dillalan Mai Suna Fuskantar Karancin Mai Sakamakon Yakin Amurka Da Iran Afrika
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
Gwamnan Jihar Adamawa Fintiri Ya Koma APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja Afrika
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Manoma Da Makiyaya: An Bukaci A Gaggauta Tantance Hanyoyin Shanu Da Iyakoki A Dukku Afrika
  • Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027 Afrika
  • ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Kama Wasu Matasa da Ake Zargin Su Da Sara Suka  Labarai
  • Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu Afrika
  • Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai
  • Haɗin Gwiwar GOSERC Da Savannah Zai Ƙarfafa Rarraba Wutar Lantarki A Faɗin Jihar Gombe Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.