Shirin Ƙara Ingancin Kiwo da Juriya na L-PRES a jihar Gombe ya ƙarfafa haɗin gwiwa da sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo ta jihar, domin ƙara inganta ayyukan da ake gudanarwa da kuma hanzarta aiwatar da ajandar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta sauya fasalin harkar kiwo a jihar.
Mai Gudanar da Shirin L-PRES na jihar Gombe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawagar shirin zuwa ziyarar sanayya ga Kwamishinan Bunƙasa Kiwo, Hon. Salihu Baba Alkali.
Farfesa Abubakar ya ce ziyarar ta kasance ne domin yi wa kwamishinan bayani kan manufofi, ayyuka da nasarorin da shirin L-PRES ya samu tun bayan fara aiki a jihar, tare da gano hanyoyin ƙara haɗin gwiwa da sabuwar ma’aikatar.
Ya bayyana cewa L-PRES shiri ne na tsawon shekaru shida da Bankin Duniya ke tallafawa, wanda jihar Gombe ta shiga a watan Disambar 2023, da nufin inganta samar da amfanin dabbobi, ƙara juriya da bunƙasa kasuwancin kayayyakin kiwo.
A cewarsa, shirin ya aiwatar da wasu muhimman ayyuka da suka shafi samar da ruwa, kasuwannin dabbobi, kiwon shanu, lafiyar dabbobi, da kuma rage rikice-rikicen manoma da makiyaya musamman a hanyoyin shanu da wuraren kiwo.
Ya ce zuwa yanzu L-PRES ya gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana sama da 100, ya gyara madatsun ruwa na gargajiya, sannan ya kafa ƙungiyoyin manoman kiwo da cibiyoyin tattara madarar shanu guda 55.
Ya ƙara da cewa shirin na samar da horo, ingantattun nau’o’in dabbobi da sauran tallafi domin ƙara yawan amfanin kiwo da ribar da manoma da masu kiwo ke samu.
Farfesa Abubakar ya kuma bayyana nasarar da shirin cusa maniyyin shanu, wato Artificial Insemination, ya samu, inda aka samu kashi 79 cikin 100 na nasarar samun ciki da kuma kashi 66 cikin 100 na haihuwa.
Ya ce wannan nasara ta sa jihar Gombe ta samu karɓuwa a matsayin abin koyi ga sauran jihohi, yayin da ake gina Cibiyar Cusa Maniyyi da Yawaita Ingantattun Nau’o’in Dabbobi a tsangayar Noma ta Jami’ar Jihar Gombe da ke Mallam Sidi.
Mai Gudanar da Shirin ya ce L-PRES na kuma tallafa wa ayyukan dakile rikice-rikice ta hanyar sake tsara da taswirar hanyoyin kiwo da wuraren kiwo, kafa wuraren hutawar dabbobi, da kuma shiga cikin kwamitocin rigakafi da sasanta rikice-rikicen manoma da makiyaya a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Ya bayyana cewa shirin na zuba jari wajen sarrafa amfanin dabbobi a cikin gida, ciki har da gina katafaren mayanka na zamani, cibiyoyin kiwon kaji da kitso, masana’antar fata da kayayyakin fata, da kuma kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa a yankin bunƙasa harkar noma da kiwo na Gombe.
Game da lafiyar dabbobi kuwa, ya ce ana gyarawa da inganta cibiyoyin kula da lafiyar dabbobi, tare da kafa dakunan gwaje-gwajen sa ido kan cututtuka da wuraren adana allurai cikin yanayin sanyi, baya ga tallafa wa shirye-shiryen yi wa dabbobi allurar rigakafi.
Farfesa Abubakar ya kuma bayyana cewa jihar Gombe ta zo ta biyu wajen gudanarwa da aiwatar da shirin L-PRES, lamarin da ya sanya wasu jihohi ke nuna sha’awar koyon darussa daga irin nasarorin da Gombe ta samu.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan Bunƙasa Kiwo na jihar Gombe, Hon. Salihu Baba Alkali, ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa da jajircewarsa wajen aiwatar da manyan ayyukan raya jihar.
Kwamishinan ya kuma taya ofishin gudanar da shirin L-PRES murnar nasarorin da ya samu, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da kiyaye inganci wajen aiwatar da ayyukan.
Ya ce kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo na da nufin ƙarfafa da kuma bunƙasa nasarorin da aka samu a fannin kiwo, musamman ta hanyar shirye-shirye irin na L-PRES.
Hon. Alkali ya ce samar da wadataccen abinci, ƙirƙirar ayyukan yi, rigakafi da sasanta rikice-rikicen manoma da makiyaya, da farfaɗo da ababen more rayuwa na kiwon dabbobi, musamman shirin cusa maniyyin shanu, na daga cikin abubuwan da ma’aikatar ta sanya a gaba.
Kwamishinan ya tabbatar wa tawagar L-PRES cewa ma’aikatar za ta ci gaba da ba shirin goyon baya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa, wayar da kan jama’a da kuma ilmantar da su, domin tabbatar da cewa al’ummar jihar sun fahimci shirye-shiryen tare da amfana da su.
Ya bayyana kyakkyawan fata cewa ƙara haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar da L-PRES zai taimaka wajen faɗaɗa tasirin shirye-shiryen kiwo, samar da wadataccen abinci, ƙirƙirar ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar Gombe.


