Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba
Published: September 6, 2026 at 7:26 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Daga Zainab Babaji a Jos

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato a Najeriya ta yi gargadi game da yadda wassu daidaikun jama’a da kungiyoyi ke amfani da na’urorin daukan hoto a sararin samaniya, wato drone, da wassu jirage marasa matuka ba bisa ka’ida ba:

Rundunar ‘yan sandan jihar tace yin amfani da jirage marasa matuka, ba tare da samun izini daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA ba, babban laifi ne.

Gargadin na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, SP Alfred Alabo.

Rundunar ta ce Najeriya na da dokoki da suka shafi zirga-zirgar jiragen sama, musamman ka’idojin zirga-zirgar jiragen sama na 2023, Sashe na 17, wanda ya shafi Tsarin Jiragen Sama na Remotely Piloted (RPAS).

A cewar sanarwar, hukumar ta NCAA ce kadai ke da alhakin bayar da izini da kuma amincewa da ayyukan jirage marasa matuka a sararin samaniyar kasar.

Ya yi gargadin cewa tilas ne a sanar da hukumar kula da harkokin jiragen sama na Najeriya wato NCAA, kwanaki sittin kafin a tada duk wata na’ura mai tashi sama.

Rundunar ta ci gaba da cewa, ana bukatar masu amfani da jirage marasa matuka da su bayar da bayanai kan wuraren da suke aiki da jadawalinsu, da kuma matakan tsaro da aka sanya wa kowane na’ura.

Ya yi gargaɗi game da yadda wassu ke amfani da irin wadannan jirage marasa matuƙa wajen yin safarar makamai ko abubuwan fashewa, da sauran ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba, wanda ka iya haifar da kisa, mummunan rauni, lalata dukiya ko muhalli, ko jefa lafiyar jama’a cikin haɗari.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bukaci masu amfani da na’urorin da su kiyaye ka’idojin tsaro na kasa da kasa, wadanda suka hada da yin shawagi a cikin iyakokin da aka kayyade, kiyaye layin hange, da kuma guje wa wuraren da ba za a iya tashi ba.

Ya kuma gargadi masu amfani da jiragen marasa matuka su guje wa yin leken asiri ba tare da izini ba, da kuma lura da cewa irin wadannan ayyukan na iya kaiwa ga cin zarafi, tsoratarwa, ko kuma yanayi da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Rundunar ta ce umarnin na da nufin karfafa tsaro a jihar Filato, da kare jiragen sama da sauran muhimman ababen more rayuwa, da kuma kara wayar da kan jama’a da bin ka’idojin gudanar da ayyukan jiragen sama.

Ta kuma yi gargadin cewa, ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su kame jiragen da masu sarrafa su da aka samu da laifin karya ka’idodi tare da gurfanar da su bisa tsarin doka.

Rundunar ta bukaci jama’a su kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

Ta jaddada cewa ba za ta bari sararin samaniyar Filato ya zama gidan wasan kwaikwayo na rashin bin doka da oda da ke iya yin illa ga tsaron lafiyar jama’a ba.

Rundunar ta ce Jama’a na iya kiran wadannan layukan sadarwa a duk lokacin da suke bukatar agajin gaggawa: 07059473022 ko 08038907662.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gombe Ta Zo Ta Biyu Wajen Aiwatar Da Shirin L-PRES
Next Post: Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
Tattaunawar Nukiliya Tsakanin Iran Da Amurka Yana Tasirin Akan Farashin Albarkatun Mai Amurka
Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki Afrika
Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
  • Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka Labarai
  • Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar Labarai
  • An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja Afrika
  • Ga Fili Ga Doki Najeriya
  • Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
  • NITDA Da GOSIDEC Sun Horar Da Ma’aikatan Gombe Don Inganta Ayyukan Gwamnati Afrika
  • An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.