Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo
Published: March 5, 2026 at 7:42 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Zaizayar kasa, da ta auku ranar Talata bayan ruwan sama mai yawa yayi sanadiyar mutuwar mutane 200 a cibiyar ma’adanin coltan ta Rubaya dake gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, a cewar ma’aikatar ma’adanai ta kasar a ranar Laraba.

Wani babban jami’i daga kungiyar ‘yan tawaye na AFC da M23 dake rike da madafun ikon Wurin hakar ma’adanin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a baya cewa mutane 5 zuwa 6 ne kawai suka rasu sakamakon zaizayar kasar.

Cibiyar ta Rubaya na samar da wajen kashi 15 cikin 100 na ma’adanin coltan a duniya, wanda ake sarrafa shi zuwa karfen tantalum, wanda ke iya daukan zafi me yawa, kuma masu kera wayoyin tarho da kwamputa da sassan jiragen sama na amfani da shi sosai.

Rubaya ta kasance karkashin ikon ‘yan tawayen ACF da M23 tun shekarar 2024. Wannan ibtila’in da ya faru ya biyo bayan wata daya da wani hatsarin a wajen yayi sandiyyar rayuwar mutane fiye da 200.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Yaki Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Ya Shiga Kwana Na Biyar
Next Post: Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage

Karin Labarai Masu Alaka

Sace Ni Bai Hana Ni Bin Hanyar Jere Ba-Ali Gantsa Labarai
Wani Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 35 A Jihar Borno Labarai
Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
Turkiyya Ta Zargi Alakar Isra’ila Da Somaliya Afrika
Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisun Najeriya Sun Amince Ta Karin Kasafin Kudi Afrika
  • Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Man Fetur A Najeriya Afrika
  • Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
  • Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Zata Binciki Kasar Iran Afrika
  • Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
  • Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.