Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sabon Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khameni Yaji Rauni Kuma Ya Nakasa
Published: March 14, 2026 at 7:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sabon shugaban addinin Islama na ran, Mojtaba Khameni, yaji rauni, kuma watakil ya nakasa, inji sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth a jiya jumma’a, har yana tababar yadda za’a yi Mojtaban ya jagoranci kasar, bayan mako biyu na hare haren da Amurka da Isra’ila suke kaiwa kan kasar.

A ranar Alhamis ne aka ji kalaman farko daga sabon shugaban addini na Iran da aka karanta a talabijin. A cikin sanarwar yayi alawashin ci gaba da rufe mashigin ruwan Hormuz, ya kuma yi kira ga kasashe makwabta su rufe dukkan sansanonin Amurka dake kasashen su, ko kuma su fuskanci kasadar Iran ta auna su a hare haren da take kaiwa.

“Iran tana da kamarori masu yawa, da na’uororin daukar magana, me yasa sai a rubuce zai yi magana, Ina ji kun san dalili. Mahaifinsa ya mutu, a tsorace yake, ko ya ji rauni, ko kuma yana kan gudu, domin ba shugaba ne halattacce ba.”

Zuwa yanzu dai babu wani hotonsa da aka gani tun harin farko da Isra’ila ta kai ya kashe iyayensa harda matarsa.

A wani mataki kuma, Amurka tana tayin bada tukuici dala milyan 10 kan duk wadda zai bata labarin ko bayanai dangane manyan jami’an soji dana leken asirin Iran, ciki harda sabon shugaban addinin kasar Ayatollah Mojtaba Khameni.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran
Next Post: Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Kawo Cikas Ga Cinikin Nama A Kenya

Karin Labarai Masu Alaka

Gombe Da UNFPA Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Yaƙi Da Cutar Fistula Da Tamowa Afrika
Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass Afrika
Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya Afrika
‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai
  • Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa Afrika
  • Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Manchester United Ta Sallami Ruben Amorim Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya Labarai
  • Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.