Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA
Published: July 19, 2026 at 8:37 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai halarci zama na 81 na Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda za a gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka a watan Satumba, inda ake sa ran zai gabatar da jawabi ga shugabannin ƙasashen duniya.

Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ya tabbatar da aniyarsa ta halartar taron tare da amincewa da dukkan shirye-shiryen da Nijeriya ta kammala domin halartar babban taron na bana.

Zama na 81 na Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya zai fara ne a ranar 8 ga watan Satumba, yayin da za a fara muhawarar shugabannin ƙasashe a mako mai zuwa.

Ana sa ran shugabannin duniya za su tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da sauyin yanayi, ci gaba mai ɗorewa, zaman lafiya da tsaro na duniya, da kuma sauran manyan ƙalubalen da ke fuskantar al’ummomin duniya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma’aikatan Jiha da Kwamishinoni 23
Next Post: CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro Afrika
Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu Afrika
Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai
Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika
Baital Malin Amurka Tace Sahannun Trump Zai Fito A Kudin Kasar Amurka
Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Layin Raba Wutan Lantarki Na Najeriya Ya Fashe Labarai
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
  • Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai Afrika
  • APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna Afrika
  • Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
  • Tattalin Arzikin Kasar Botswana Zai Farfado Afrika
  • Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.