Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Amince Da Gyaran Fadar Sarkin Gombe
Published: August 9, 2026 at 10:28 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranci taron majalisar haɗin gwiwa kan ayyukan ci gaban jihar, wanda shi ne karo na takwas, domin duba yadda ake tsara da aiwatar da ayyukan raya jihar cikin tsari da inganci.

Taron, wanda shi ne na farko tun bayan kafa ƙananan hukumomin ci gaba guda 13 (LCDAs), ya mayar da sabbin hukumomin cikin tsarin tsare-tsaren ci gaba da aiwatar da ayyukan gwamnati a jihar.

Da yake bayyana sakamakon taron, Darakta-Janar na Hukumar Haɗin Gwiwar Ayyukan Ci Gaba da Muhimman Ayyuka ta Jihar Gombe (JPDESA), Dr. Mahmood Yusuf ya ce majalisar ta amince da wasu muhimman ayyuka da ƙarin ayyukan more rayuwa domin magance buƙatun da suka taso a fannonin ci gaban jihar.

Daga cikin manyan abubuwan da majalisar ta amince da su akwai inganta da gyara Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III, CFR.

Bldr. Mahmoud Yusuf ya ce matakin na cikin ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya na kare da inganta muhimman cibiyoyin gargajiya, tare da samar musu da abubuwan more rayuwa da suka dace da matsayinsu.

Ya ƙara da cewa inganta fadar zai taimaka wajen ƙawata muhalli, inganta ayyukan fadar da kuma samar da yanayi mai kyau ga harkokin gudanarwa.

A cewarsa, matakin ya kuma nuna irin muhimmancin da gwamnatin jihar ke bai wa sarakunan gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kan al’umma da kuma tallafa wa manufofin gwamnati na ci gaba.

A wani mataki kuma, majalisar ta amince da samar da ƙarin muhimman abubuwan more rayuwa a sabbin ƙananan hukumomin ci gaba guda 13, domin tabbatar da cewa sun fara aiki cikin sauƙi da inganci.

Darakta-Janar ɗin ya bayyana cewa duk da cewa an kammala samar da gine-ginen sabbin ƙananan hukumomin, gwamnati ta ga ya dace a ƙara wasu muhimman kayan aiki da ayyuka domin ba su damar fara gudanar da ayyukansu ba tare da tsaiko ba.

Daga cikin abubuwan da aka amince da samarwa akwai na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da kuma na’urorin sa ido na tsaro, baya ga sauran muhimman kayan more rayuwa.

Ya ce samar da wutar lantarki ta hasken rana zai taimaka wajen tabbatar da samun ingantaccen wutar lantarki a sabbin cibiyoyin, yayin da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana za su samar da ruwa mai ɗorewa ga ma’aikata da sauran masu amfani da cibiyoyin.

Ya ƙara da cewa na’urorin sa ido na tsaro za su taimaka wajen ƙarfafa tsaro, kare kadarorin gwamnati da kuma samar da ingantaccen yanayi ga ma’aikata da al’ummar da za su riƙa amfani da ayyukan sabbin ƙananan hukumomin.

Majalisar ta kuma yi nazari kan ayyukan raya jihar da ake ci gaba da gudanarwa, tare da duba wasu ƙarin matakan da ake buƙata domin tabbatar da ci gaba da samun nasarar ayyukan raya jihar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
Next Post: Newcastle Na Dab Da Kammala Yarjejeniyar Daukar Højbjerg Daga Marseille Kan €15m

Karin Labarai Masu Alaka

SCSN Ta Yi Kira Ga Hukumomi Su Tabbatar Da Bin Doka A shari’ar El-Rufa’i Afrika
Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Rasuwar Tsohon Shugaban NUJ FCT, Osambedwan, Babban Rashi Ne — Ferfesa Alkali Afrika
Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NDLEA Ta Fara Binciken Kwakwaf Akan Wasu ‘Yan Mata Dake Kai Kwaya Gidan Yari Labarai
  • Mutane Kusan 30 Ne Suka Mutu a Nguru Dake Jihar Yobe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Maganganun Jami’an Shige Da Fice Dana Shugaban Kasa Trump Suna Cin Karo Da Juna Amurka
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
  • Harin ‘Yan Daba Ya Hallaka Mutane 70 A Kasar Haiti Labarai
  • Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe Afrika
  • Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.