Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi
Published: April 14, 2026 at 8:19 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dakarun Amurka ta ruwa a ranar Litinin suka fara killace hanyoyin ruwa na kasar Iran, tare da hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin ruwa na kasar, inji shugaba Donald Trump, Iran tayi barazanar zata rama kan kasashe makwabta a yankin Gulf, bayanda aka tashi baram baram a shawarwari da suka yi a Pakistan, da nufin kawo karshen yakin da suke gwabzawa.

Wani jami’in Amurka yace ana ci gaba da tuntubar juna da Iran, da nufin cimma yarjejeniya. Shi ma Prime Ministan Pakistan Shehbaz Sharif yace ana ci gaba da kokarin warware rikicin.

Saboda wannan yanayi da ake ciki, farashin mai ya sake cullawa sama da dala dari kan ko wace ganga, ba tare da an ga wata alamar za’a bude mashigin ruwa na Hormuz nan take ba, domin sassauta kassara jigilar mai mafi girma a tarihi, da kuma ci gaba da nuna damuwa kan dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta na mako biyu da aka cimma cikin makon jiya.

Trump ya fada a jiya Litnin cewa Iran ta yi tuntuba a jiyan tana son a kulla yarjejeniya, amma ba zai amince da duk wata yarjejeniyar da zata kyale Iran ta mallaki makaman Nukiliya ba.

Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare hare akan Iran ranar 28 ga watan Febwairu, Iran ta rufe mashigin ruwa na Hormuz ga dukkan jiragen ruwa in banda nata, tana mai cewa ba jirgin ruwan da za’a kyale ya wuce ba tare da izininta ba tare da an biyan wani hasafi.

Trump yace Washington zata hana duk wani jirgin ruwa daga Iran, da duka jiragen da suka biya Farisa wani kudi wuce wa, kuma duk wani karamin jirgin ruwan Iran masu kai hari da ya yi kusa da jiragen ruwa yaki na Amurka zai zama tarihi.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye
Next Post: Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba

Karin Labarai Masu Alaka

An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu Afrika
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
Tinubu Ya Jaddada Buƙatar Kare Rayukan ‘Yan Afirka A Taron ECOWAS Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
  • Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jihar Ekiti Ta Aiwatar Da Dokar Haraji Najeriya
  • Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya Amurka
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • An Saka Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Lamurde Jihar Adamawa Tsaro
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
  • Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.