Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka
Published: March 25, 2026 at 4:34 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar talata a New York, shugaban kasar Ghana, John Daramani Mahama, ya soki manufofin gwamnatin Amurka, kan abunda ya kira amincewa da goge tarihin bakar fata, yana mai cewa hakan zai iya shafar wasu lamura sosai.

Tun bayan da ya dawo kan madafun iko, shugaba Donald Trump, ya auna hukumomi da cibiyoyin al’adun gargajiya, da suka hada da wuraren adana tarihi da wasu kayan al’adu, domin cire abunda ya kira “manufofin nuna kiyayya ga Amurka.”

Kalaman shugaba Trump da wasu dokokin shugaban kasa, da ake kira Executive orders, sun kai ga cire wasu kayan tarihin bautar da bakar fata, sake dawo da kayan tarihin turawa masu da’awar wariya, da wasu matakai da masu yakin tabbatar da ‘yancin tsiraru suke ganin zai maida hanun agogo baya.

Wadan nan matakai sun zama manhaja ga wasu gwamnatoci da kungiyoyi ko kamfanoni masu zaman kansu,” inji shugaba John Daramani, lokacin da yake magana a wani lamari a MDD, yace ko babu komi sannu a hankali matakan suna halatta goge tarihi.

Shugaba Mahama yace a Amurka ana cire kososhi da suke koyar da tarihin bakar fata a makarantu, ana tilastawa cibiyoyi su daina koyarda “gaskiyar tarhin bauta da wariyar launin fata,” kuma littatafai da suke karantar da wannan batu ana ci gaba da haramta su.

Shugaba Mahama a bara, ya amince da wani shirin karbar ‘yan asalin Afirka ta yamma da gwamnatin Trump ta tusa keyar su, a baya ya soki shugaba Trump kan karyar da yayi cewa ana yiwa turawa kisan kare dangi tare da kwache musu filaye a Afirka ta kudu, da cewa fadin hakan cin fuska ne ga daukacin Afirka.

Fadar White House bata maida martani nan take kan maganar shugaba John Daramani Mahama.

Afrika, Amurka, Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Dillalan Mai Suna Fuskantar Karancin Mai Sakamakon Yakin Amurka Da Iran
Next Post: Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique Afrika
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu Afrika
  • An Damke Wani Likita Da Ke Taimakawa ‘Yan-Ta’adda Najeriya
  • Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
  • Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
  • Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Amince Da Tsagaita Wuta Labarai
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.