Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Amurka Tana Ganawa Da Manyan Jami’an Leken Asiri
Published: January 30, 2026 at 9:57 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A cikin makon nan gwamnatin shugaba Trump tana ganawa da manyan jami’an tsaron aikin leken asiri daga Isra’ila da saudiyya, a Washington DC domin tattaunawa a zama daban daban game da Iran, yayinda shugaba Trump yake tunanin kaiwa Farisan farmaki, kamar yadda wasu majiyoyi da suke da sanayya kan lamarin suka fada.

Zaman dar dar ya karu a gabas ta tsakiya sakamakon jibge kayan yaki a yankin da Amurka take yi. Ranar laraba shugaba Trump yayi kira ga Iran ta hanzarta zuwa teburin shawarwari kan shirin Nukiliyar kasar, ko ta fuskanci farmaki daga Amuka. Wanda yasa Iran kuma tayi barazanar daga Iran cewa zata maida martani mai tsanani idan aka taba ta.

Kamar yadda wasu kafofin yada labarai na Amurka suka bayyana, babban jami’in aikin leken asiri na Isra’ila Janar Shlomi Binder, yayi shawarwari da jami’an Amurka a ma’aikatar tsaro ta Pentagon, da CIA, da kuma fadar White House a ranakun talata da laraba, inda ya gabatar da bayanai kan wasu muhimman wurare da Amurka zata iya aunawa idan ta tsaida shawarar kai wa Iran din hari.

Haka nan shima Ministan harkokin tsaro na Saudiyya Yerima Khalid Bin Salman, yana Birnin Washington domin gudanar da shawarwari da Washington akan batun na Iran.

Saudiyya da wasu kasashe da suke yankin Gulf, sun nemi sassauta lamarin domin kaucewa yaki da zai shafi yankin na gabas ta tsaiya baki daya.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Sojan Burkina Faso Ta Soke Jam’iyyun Siyasar Kasar
Next Post: An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya

Karin Labarai Masu Alaka

Prime Ministan Pakistan Yace Zai Karbi Bakoncin Tattaunawar Amurka Da Iran Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Rundunar Sojin Amurka Sunfara Ficewa Daga Kasar Sham Amurka
Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran Afrika
Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Afrika
Netanyahu Ya Umarci Rundunar Sojoji Takara Fadada Ayyukanta A Lebanon Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Babban Bankin Najeriya Ya Rage Kudin Ruwa Da Kashi Daya Cikin Dari Labarai
  • Azumin Ramadan Yahadu Da Azumin Lent Da Mabiya Addinin Kirista Sukeyi A Wannan Shekarar Labarai
  • An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi Afrika
  • Sojin Israela Sunkai Hari Kan Falatsinawa Tsaro
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.